Rigima da Soja: Kungiya Ta Bukaci Tinubu Ya Kori Wike, Ta Fadi Wanda Ya Kamata Ya Maye Gurbinsa
- Ana ci gaba da muhawara kan takaddamar da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi da wani jami'in sojan ruwa
- Kungiyar COCTA ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kori Wike daga mukaminsa saboda kunyata gwamnatinsa
- Hakazalika, ta ta ba shugaban kasan shawarar mutumin da ya kamata ya maye gurbin tsohon gwamnan na jihar Rivers
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Conference of Civil Society for Transparency and Accountability (COCTA) ta ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shawara.
Kungiyar COCTA ta bukaci Shugaba Tinubu da ya sauke ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, saboda rigimar da ya yi da wani jami’in rundunar sojojin ruwa a Abuja.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa da wayar da kai na COCTA, Haruna Abdulsalam, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, 15 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
Shugaban NIWA ya yi murabus daga mukamin da Tinubu ya nada shi, zai nemi takarar gwamna
Kiran COCTA ya zo ne bayan wani bidiyo da ya nuna Wike yana takaddama da jami’in sojan ruwa a wani filin da ake takaddama kansa a Abuja ya bazu a shafukan sada zumunta a ranar 11 ga Nuwamba.
Kungiya ta ce Wike ya kunyata Tinubu
Kungiyar ta ce wannan takaddama abin kunya ce ga gwamnatin Tinubu da kasa baki daya.
COCTA ta ce an nada jami’an gwamnati ne domin kare martabar gwamnati, ba domin tsoratar da jami’an tsaro da ke aiwatar da abin da doka ta tanada ba.
Sanarwar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya kan zargin mayar da daruruwan filaye a Abuja zuwa gidajen zama, otel-otel da manyan wuraren kasuwanci.
“Ya kamata wannan bincike ya duba batun soke mallakar filaye ta hanyar da ba ta da tushe, musamman wadanda ake zargin suna amfanar da iyalai da abokan manyan mutane, da kuma sayar da filayen gwamnati da aka ware domin asibitoci da ayyukan jama’a ga masu zaman kansu."
“Wasu daga cikin wadannan filaye ana sayar da su ne a biliyoyi, a biya da kuɗin waje, kuma muna da hujjoji, kwafe-kwafen koke-koke da bayanan filayen da aka soke, da ke nuna yadda ake cin hanci da amfani da dukiyar jama’a don son kai.”
- Haruna Abdulsalam
COCTA ta ce dole a hukunta wadanda suke da hannu, tare da kare filaye da dukiyar jama’ar Abuja domin al’umma gaba daya.

Source: Facebook
Wa ake so ya maye gurbin Tinubu?
Kungiyar ta kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya sauya Wike da Injiniya Tein Jack-Rich, ɗan asalin jihar Rivers kuma mamba na APC.
COCTA ta ce Jack-Rich ya cancanci wannan kujera saboda ya na da zurfin sanin lamurran al’umma, ci gaban birane da hidimar jama’a.
Ta jinjinawa fitattun ‘yan Najeriya kamar lauyan kare hakkin dan-Adam, Femi Falana, da ministan tsaro, Mohammed Badaru, da Matawalle, bisa tsayuwarsu akan gaskiya wajen kin amincewa da duk wani dalili da zai sa a hukunta jami’in sojan da ya yi takaddama da Wike.
PDP ta kori Nyesom Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta dauki matakin ladabtarwa kan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan
Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja
Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike, tare da wasu daga cikin jiga-jiganta saboda laifuffuka daban-daban.
Daga cikin sauran wadanda aka kora akwai tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Samuel Anyanwu wanda shi ne tsohon sakataren jam’iyyar.
Asali: Legit.ng
