'Ba Sani ba Sabo': Marwa Ya Yi Magana bayan Tinubu Ya Sake Nada Shi Shugaban NDLEA

'Ba Sani ba Sabo': Marwa Ya Yi Magana bayan Tinubu Ya Sake Nada Shi Shugaban NDLEA

  • Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya gargadi manyan masu safarar kwayoyi cewa za su gamu da kunci a wa'adinsa na biyu
  • Marwa ya ce sabon wa’adin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi zai kawo karshen ƙungiyoyi ko mutanen da harkar kwayoyi
  • Shugaban ya yi kira ga masu safarar kwayoyi da masu noman wiwi su shiga taitayinsu ko su rasa dukkan dukiyarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (rtd.), ya sake fitar da sabon gargadi ga manyan dilolin kwayoyi da ƙungiyoyin safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

A ranar 14 ga Nuwamba, 2025, muka ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sake nada Marwa matsayin shugaban NDLEA, inda zai sake yin wasu shekaru biyar a kujerar.

Buba Marwa ya ce zai kuntatawa 'yan shaye-shaye bayan Tinubu ya sabunta nadinsa.
Hoton Buba Marwa, shugaban hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA). Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Buba Marwa ya gargadi masu sha da fataucin kwayoyi ne a yayin da ya isa ofishin hukumar a Abuja, inda jami’ai suka tarbe shi cikin murna nadin da aka yi masa.

Kara karanta wannan

'Ka da a ziyarci kabarina': Tsohon gwamna ya ba da wasiyyar yadda za a birne shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marwa ya ce wa’adi na biyu ba zai yi sauƙi ba

Yayin jawabi ga ma’aikatan da suka tarbe shi cikin murna, Marwa ya ce dawowarsa a ofis na nufin sabuwar manuniya ta karin matakai masu tsauri a kan ’yan safarar kwayoyi.

Buba Marwa:

“Za mu matukar tsananta masu a wannan wa’adin namu na biyu. Ba za mu bari a rika safarar kwayoyi ba — ko shigowa ko fita ko yawo a cikin Najeriya.”

Ya ce abin mamaki ne ganin irin taron maraba da jami’an NDLEA suka masa bayan dawowarsa daga sallar Juma’a, yana mai yaba wa ma’aikatan bisa nuna kauna da ƙwazo.

Godiyarsa ga shugaban kasa da jami’an NDLEA

Marwa ya godewa Shugaba Tinubu, da ma’aikatan NDLEA, yana mai cewa wannan sabon wa’adi wata babbar amana ce da za ta ƙarfafa yaki da miyagun kwayoyi.

Shugaban na NDLEA ya ce:

“Muna godiya ga shugaban kasa saboda wannan girmamawa da kuma sabuwar amanar da aka sake dora mana. Ina godiya ga ma’aikatan NDLEA maza da mata da ke hidima dare da rana duk da haɗarin da ke tattare da aikin.”

Kara karanta wannan

'Yan majalisar dokoki sun tsawaita wa'adin shugaban kasa a Benin

Ya kara da yaba wa manyan jami’an gwamnati da abokan hulɗa na ƙasashen waje bisa ci gaba da tallafi da haɗin gwiwa wajen magance matsalar kwayoyi a Najeriya.

Buba Marwa ya sake zama shugaban hukumar NDEA a karo na biyu.
Hoton Buba Marwa, shugaban hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA). Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

Marwa ya gargadi ’yan safarar kwayoyi

A wani bangare na jawabin nasa, Marwa ya aika da sako kai tsaye ga masu safarar kwayoyi da masu noman wiwi a ƙasar.

“Yanzu ne lokacin da ya dace su bar wannan haramtacciyar sana’a su koma abin da yake halal,” in ji Marwa.

Ya tuna da sashen Alternative Development na NDLEA da ke taimaka wa mutanen da ke son komawa sana’o’in halal, amma ya gargadi masu dagewa kan aikata laifi cewa hukuma ta shirya tsananta musu.

“Duk wanda ya ƙi barin wannan mummunar sana’a, ya sani cewa NDLEA a shirye take, kuma za mu aiwatar da doka. Za a kama ku, a kwace kwayoyi, a kuma kwace dukiyar da kuka tara. Kuma idan kun fito daga gidan yari, ba za ku tarar da komai ba.”

- Buba Marwa.

An tsinci gawar shugaban NDLEA a otel

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu gawar shugaban hukumar NDLEA reshen jihar Cross River a dakin otal wanda ya tayar da hankali matuka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da sake nada Buba Marwa shugaban NDLEA zuwa 2031

An rahoto cewa an tsinci gawar Morrison Ogbonna a wani otal da ke Calabar, babban birnin jihar, a ranar Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025.

Abokan aikinsa da suka zo daukarsa sun ce sun buga ƙofa sau da yawa ba tare da amsa ba, daga bisani aka same shi matacce a kan gadon dakin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com