‘Ka da a Ziyarci Kabarina’: Tsohon Gwamna Ya ba da Wasiyyar Yadda Za a Birne Shi

‘Ka da a Ziyarci Kabarina’: Tsohon Gwamna Ya ba da Wasiyyar Yadda Za a Birne Shi

  • Tsohon Gwamna Ayodele Fayose ya ba da umarni kan yadda yake son a birne shi bayan ya yi bankwana da duniya
  • Fayose ya yi gargadi ga masu zuwa kabarin mutane bayan sun rasu inda ya ce yana son a birne shi cikin makonni huɗu
  • Shugabanni da dama sun taya shi murna yayin bikin cikar sa 65, ciki har da Gwamna Biodun Oyebanji da ya yaba da gudunmawarsa ga jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ba da wasiyya game da yadda za a birne shi bayan Allah ya karbi rayuwarsa.

Fayose ya bayyana cewa yana so a binne shi cikin mako hudu kacal bayan rasuwarsa, tare da yin cikakkiyar umarni kan yadda ake son a gudanar da jana’izarsa.

Kara karanta wannan

Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja

Tsohon gwamna ya fadi yadda yake son a birne shi
Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose. Hoto: Ayodele Fayose.
Source: Facebook

Tsohon gwamna ya bada wasiyya ga na baya

Fayose, wanda ya cika shekara 65, ya bayyana haka ne cikin wani bidiyon mintuna shida da aka wallafa a YouTube.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Ekiti ce kawai za ta kula da gawarsa da dukkan shirye-shiryen binne shi.

Ya kara da cewa ko yaushe mutuwar ta faru, gwamnati ce za ta karɓi ragamar al’amarin.

Ya ce:

“Mutuwa dole ce. Gawata ta gwamnati ce. Na rubuta wa gwamna wasiƙa.”
“Ko cikin shekara 20, 30 ko 15, duk lokacin da Allah ya nufa, gwamnati ce za ta ɗauki gawata. Kuma dole a binne ni cikin makonni huɗu, domin gwamnati na iya buƙatar lokaci kafin ta shirya.”
Fayose ya ba da wasiyya kan yadda za a birne shi
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose. Hoto: Ayodele Fayose.
Source: Depositphotos

Umarnin da Ayo Fayose ya ba 'ya'yansa

Fayose ya ce ’ya’yansa su sanya kayansu na yau da kullum, su kuma bi umarnin gwamnati lokacin binne shi.

Game da kabarinsa, ya ce a binne shi a gidan kakarsa, inda ya riga ya shirya lambu tun tuni, ya kuma ce dole ne a daina zuwa wurin bayan an binne shi.

Kara karanta wannan

ADC ta yi mamakin matakin da Tinubu ya dauka bayan sabanin Wike da A.M Yerima

A kalamansa:

“Ku bar ni in huta. Idan kuna son nuna min kauna, ku nuna min yanzu da ina raye, ba bayan na tafi ba.”

Hakanan, an yada wani bidiyon mintuna 20 da ke nuna fitaccen mawaki King Sunny Ade yana raira waka ga Fayose yayin bukin godiyar cikarsa shekara 65.

Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya taya shi murna ta bakin mai magana da yawunsa, Yinka Oyebode, inda ya yaba da gudunmawarsa ga jihar, yana mai cewa:

“Jagora ne mai kaunar jama’a, kuma gwarzon siyasar kasa wanda baya jin tsoron faɗin ra’ayinsa.”

'Matata ta hana ni sukar Buhari' - Fayose

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce matarsa ta hana shi sukar Muhammadu Buhari bayan mutuwarsa a watan Yulin 2025.

Fayose ya bayyana cewa ba zai iya yabon mamaci ba idan bai tabuka komai ba, yana mai cewa Najeriya na cikin matsaloli tun zamanin Buhari.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Amaechi ya fadi tattaunawarsu da Amurkawa kan 'kisan' Kiristoci

Ya kare Bola Tinubu, yana cewa yana da saukin kai kuma ya gaji tattalin arziki mai rauni a Najeriya bayan shiga ofis a watan Mayun 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.