‘Sai Mun Biya’: Al’umma Sun Fadi Makudan Kudi da Suke ba ’Yan Bindiga domin Kariya
- Al’ummomi sun shiga tsoro sosai sakamakon yawaitar garkuwa da mutane, satar babura da kuma ayyukan kungiyar asiri
- Mazauna wasu yankuna a Benue suna samun kira daga miyagu da ke bukatar kuɗi tare da barazanar yin garkuwa da su
- ’Yan yankin suna kira ga gwamnati da jami’an tsaro su ba tallafi, domin tsaro ya tabarbare kuma mutane ba sa iya zirga-zirga
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Mazauna yankin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue sun shiga cikin tsananin fargaba game da hare-haren yan bindiga.
Hakan ya biyo bayan karuwar laifuffuka sosai a kwanakin baya, ciki har da barazanar garkuwa da mutane.

Source: Original
Fargabar da al'umma suke ciki kan yan bindiga
Rahoton Vanguard ya ce mutanen na fuskantar satar babura da kuma ayyukan ƙungiyoyin asiri a cikin garin.

Kara karanta wannan
Sulhu da 'yan bindiga: Sheikh Gumi ya ragargaji masu sukarsa, ya fadi nasarorin da ya samu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi daga yankin sun shaida cewa mutane da dama suna samun kira daga wasu mutane da ba a sani ba, suna neman kuɗi tare da barazanar cewa za su yi garkuwa da wanda bai biya ba.
A cewarsu:
“Mutane suna tsoro saboda masu kiran suna magana cikin tsari kamar suna da cikakken shirinsu. Muna bukatar taimako kafin lamarin ya fi ƙarfinmu.”
An kuma bayyana cewa rashin tsaro ya ƙara tsananta ne saboda ayyukan wata ƙungiyar asiri da ake zargi, wacce ake cewa tana gudanar da tarurrukanta a wani shago.
Majiyar ta ce:
“Wadannan samari suna yin taro da rana da dare. Ayyukansu suna tayar da hankali, kuma kowa yana tsoron me suke shirin yi.”

Source: Facebook
Yawan sace-sace da ake yi a Benue
Har ila yau, satar babura ta yi kamari a yankin cikin makonni, inda barayi ke kai wa direbobi hari da dare, cewar Sahara Reporters.
Wannan lamari ya saka mutane da yawa gaba ɗaya daina fita da dare saboda tsananin tsoro wand ake dakula lamuran yan yankin.
Daya daga cikin mazauna ya ce barazanar garkuwa ta kai wani mataki mai muni, ya ce wani mai POS ya biya har N100,000, bayan da yan bindiga suka gargade shi cewa za su yi garkuwa da shi idan ya ƙi.
Mutane sun roki gwamnati da jami’an tsaro su shigo cikin gaggawa, saboda lamarin na tabarbarewa kuma yana iya rikidewa zuwa babban bala’i idan ba a dakatar ba.
Wani mazaunin ya ce:
“Muna kira da gwamnati da ‘yan sanda su taimaka mana. Rayuka da dukiyoyi ba su da tsaro yanzu, kuma mataki na gaggawa ya zama dole.”
Dan Makurdi ya yi magana da Legit Hausa
Terfa Favour David ya bayyana cewa tabbas yankunan da dama suna cikin mayuyacin hali wanda yanzu ba su iya ziyartarsu.
Ya ce:
"Yanzu na shafe lokaci mai tsawo ba na zuwa kauyenmu saboda halin da suke ciki a yanzu na hare-haren yan bindiga."
Ya bukaci hukumomi da su yi gaggawar kawo karshen matsalolin inda ya ce bai kamata ana wasa da rayukan al'umma ba.
An rasa rayuka a rikicin manoma, makiyaya
Mun ba ku labarin cewa mutane sun rasa rayukansu yayin da aka kai harin ramuwar gayya a kauyen Anwule da ke karamar hukumar Ohimini a Benue.
Harin ya biyo bayan kisan wani makiyayi da ake zargin wasu mazauna kauyen suka aikata a ƙarshen watan Agustan 2025.
Mahukunta sun kai ziyara yankin, inda suka roƙi jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

