Abin Takaici: Yan Bindiga Sun Harbe Tsohon Dan Takarar Majalisar Tarayya a Zamfara

Abin Takaici: Yan Bindiga Sun Harbe Tsohon Dan Takarar Majalisar Tarayya a Zamfara

  • Rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da ta'azzara yayin da aka kashe babban dan siyasa
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe tsohon dan takarar Majalisar Tarayya a kan hanyar Tsafe, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma
  • An bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mutum mai kishin yankin da cewa rasuwarsa babban gibi ce ga jama’ar Shinkafi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - An tabbatar da rasuwar wani dan siyasa a jihar Zamfara bayan harin yan bindiga.

Majiyoyi sun tabbatar da marigayin ya hadu da ajalinsa ne a kan hanyar Tsafe da ke jihar a yankin Arewacin Najeriya.

Yan bindiga sun kashe dan siyasa a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan bindiga sun hallaka dan siyasa a Zamfara

Mun samu wannan rahoto ne daga Barden Shinkafi, Abdul Kadir Aliyu wanda ya wallafa a Facebook a yau Asabar 15 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

An bindige matashi a wajen jana'izar mahaifinsa bayan turnukewa da harbe harbe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu ya ce Hon. Umar S. Fada Moriki ya rasa ransa ne bayan wasu ’yan bindiga sun kai masa hari a kan hanyar Tsafe, inda suka kashe shi.

Marigayin ya shahara wajen himma da gaskiya a ayyukansa, musamman kokarinsa na ganin yankin Shinkafi da Zurmi sun ci gaba cikin kwanciyar hankali da cigaba.

Dr. Abdul Kadir Aliyu Shinkafi ya jajanta wa iyalan mamacin, yana rokon Allah ya jikansa, tare da kira da a kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

A cikin rubutunsa, Abdul ya ce:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
"Yau mun samu labarin rasuwar tsohon ɗan takarar Majalisar Tarayya na Shinkafi/Zurmi, Hon. Umar S. Fada Moriki, wanda wasu miyagun barayi suka kashe a kan hanyar Tsafe da safiyar yau. Wannan lamari abin takaici ne, abin bakin ciki, kuma babban rashi ga al’umma baki ɗaya.
"Hon. Umar ya kasance mutum mai gaskiya da jajircewa wajen fafutukar ganin an samu ci gaba da walwala a yankinmu. Rashinsa ya bar babban gibi da ba za a iya cike shi da sauƙi ba."

Kara karanta wannan

Rawar da Bola Tinubu ya taka a rikicin Wike da soja, A.M Yerima

Wasu yan bindiga sun kashe tsohon dan takarar majalisar tarayya
Marigayi Hon. Umar S Fada da yan bindiga suka hallaka. Hoto: Malam Murtala Bello Sokoto.
Source: Facebook

Sakon ta'aziyya da addu'o'i ga marigayin

Har ila yau, Barden Shinkafi ya tura sakon ta'aziyya na musamman ga iyalan marigayin inda ya yi masa addu'ar samun rahama.

Ya kara da cewa:

"A madadin kaina da iyalaina tare duk magoya bayana muna mika ta’aziyya ga iyalansa, ’yan uwa, abokai da al’ummar Shinkafi da Zurmi, Allah ya jikan shi, ya amshi rayuwarsa da rahama, ya ba iyalansa hakuri da juriya.
Muna rokon Allah ya kawo ƙarshen wannan ta’addanci da kashe-kashen da suka addabi al’ummarmu."

Yan bindiga sun farmaki dan majalisar tarayya

Mun ba ku labarin cewa wani soja ya rasa ransa yayin da jami'an tsaro suka mayar da martani ga harin da yan bindiga suka kai kan dan majalisar tarayya.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Lumma–Babanna da ke Borgu a jihar Niger inda mutane da dama suka jikkata.

Shaidu sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun lalata akalla motocin tawagar dan siyasar 11 da harbin bindiga wanda ya raunata mutane.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.