Kalaman Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas Sun Tayar da Kura, Ya Fito Ya ba da Hakuri
- Mutanen karamar hukumar Fagge a jihar Kano sun nuna bacin ransu bisa wasu kalamai da shugaban APC, Abdullahi Abbas ya fada
- Hakan ya sa wasu mutum 10 suka maka shi a gaban kotun majistire da ke cikin Kano bisa zargin yunkurin tayar da fitina
- Abdullahi Abbas ya fito ya ba mutanen Fagge hakuri, yan mai bayyana cewa an yi masa gurguwar fahimta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya nemi afuwar mazauna Fagge bayan kalamansa sun haifar da ce-ce-ku-ce da harzuka wasu mutanen yankin.
An ruwaito cewa kalaman Abdullahi Abbas sun harzuka wasu daga cikin shugabannin al'umma a Fagge, kuma har sun kai kara gaban kotu.

Source: Facebook
A cikin sautin murya da lauyan mazauna Fagge, Barista Abba Hikima Fagge, ya wallafa a Facebook, Abdullahi Abbas ya ce an yi kuskuren fahimtar maganarsa.

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina da malamai na addini da na siyasa, abokai na kut-da-kut da amintattu a karamar hukumar Fagge, babu abin da zai sa in ci mutuncin mutanen Fagge. Ina neman afuwar ku.”
Kalaman Abdullahi Abbas sun harzuka mutane
Leadership ta ruwaito cewa neman afuwar ya zo ne bayan mutane 10 daga Fagge sun shigar da ƙorafi a Kotun Majistare, suna zargin shugaban APC da yin kalamai masu tayar da fitina da bata sunan al’ummar yankin.
Masu ƙara sun hada da Dr. Nuruddeen Abubakar, Sheikh Abubakar Ya’u, Alhaji Sani Salisu, Alhaji Mustapha Rabiu, Sheikh Auwal Isa, Ubaidullahi Ibrahim da Malam Auwal Sabiu.
Sauran su ne Nafiu Shu’aibu Hikima, Malama Aisha Ibrahim, da Malam Ali Muhammad, kuma sun shigar da ƙarar ne “a madadin kansu da sauran mutanen Fagge masu son zaman lafiya."
An nemi kotu ta sa a kama shugaban APC
A cikin bukatar da suka gabatar a gabn kotu, sun roki kotu ta bayar da umarnin kama Abdullahi Abbas tare da umurta kwamishinan ‘yan sanda ya bincike shi.
Sun kafa hujja da sashe na 107 da 126(a) na Dokar Gudanar da Hukunce-Hukuncen Laifuka ta Jihar Kano (ACJL) ta 2019.
Tuhume-tuhumen da masu kara suka shigar kan shugaban APC sun hada da cin mutunci da gangan, saka kiyayya tsakanin al’umma, bata suna da tunzura jama’a.
Wadanda kalaman shugaban APC ya fada?
Tun farko an ji Abdullahi Abbas cikin wani taron siyasa yana cewa “duk wani marar amfani” za a danganta shi da Fagge, tare da wasu karin kalamai da aka ɗauka a matsayin masu tada hankali da raina doka.
Duk da cewa shugaban APC ɗin ya dage cewa an fassara maganarsa ba daidai ba, al’ummar Fagge sun ce kalaman sun yi tsauri, kuma suna iya haddasa rabuwar kai a cikin jama’a.

Source: Facebook
Ana sa ran kotu za ta yanke hukunci kan bukatun nan da kwanaki masu zuwa. Ammma Abdullahi Abbas ya fito ya ba da hakuri.
Wani dan Kano, Aminu Yusuf ya ce duk da yana da banbancin siyasa da Abdullahi Abbas, amma abin da ya yi na ba da hakuri abu ne mai kyau kuma ya nuna dattako.
Matashin ya shaidawa Legit Hausa cewa bai taba tunanin dan Sarki zai iya ba da hakuri ba ko da kuwa ya yi katobara irin wannan.
"Gaskiya ya nuna nagarta a haka, ni a yadda na san shi ban ma yi tunanin zai bada hakuri ba, amma abin da ya yi shi ne daidai, kuma na san wadanda suka dauki zafi za su sauka," in ji shi.
Abba na shirin gabatar da kasafin 2026
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin gabatar da kasafin kudin da zai lakume akalla Naira tiriliyan daya a 2026.
Gwamna Abba ya tabbatar da cewa da zaran an kammala tsara kasafin kudin na shekarar 2026, zai gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin jihar Kano.
cewarsa, an samu karin kudin kasafin ne sakamakon bunkasa hanyoyin tara kudaden shiga na cikin gida da kuma rufe duk wata hanyar ɓarna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

