An Fadi Gaskiya kan Ikirarin Sace Birgediya Janar yayin Gwabzawar Sojoji da ISWAP

An Fadi Gaskiya kan Ikirarin Sace Birgediya Janar yayin Gwabzawar Sojoji da ISWAP

  • An yada wasu rahotanni da ke ikirarin cewa wasu 'yan ta'adda sun kaiwa sojojin Najeriya farmaki a yankin Damboa na jihar Borno
  • Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 1:30 zuwa 4:00 na rana, ba cikin dare ba kamar yadda aka yada a farko
  • Kwandan sojoji, Birgediya Janar M. Uba da aka ce an sace ya fito cikin bidiyo ya bayyana halin da ya ke ciki bayan farmakin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Wani rahoton karya da ya bazu a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa mayakan ISWAP sun yi wa sojojin Najeriya kwanton-bauna a Damboa.

Labarin ya ce 'yan ta'addan sun kashe da dama cikin jami'an tsaro tare da sace kwamanda da wasu dakaru.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun ga ta kansu: Hafsan sojojin sama ya sha alwashi kan rashin tsaro

Wasu dakarun sojojin Najeriya
Shugabannin sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: Nigeria Air Force HQ
Source: Facebook

Sai dai sakamakon binciken da Zagazola Makama ya fitar a X ya tabbatar da cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken ya tabbatar cewa babu wani babban jami’in soja da aka sace, kuma harin bai faru cikin duhu ko cikin dare ba kamar yadda ake yadawa.

A maimakon haka, an tabbatar cewa harin ya faru ne da rana, tsakanin ƙarfe 1:30 zuwa 4:00, a kan hanyar MSR Burum–Kubua kusa da Azir/Wajiroko a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Hakikanin abin da ya faru a harin Damboa

Bisa ga bayanai na gaskiya da aka samu, sojojin suna kan aiki ne lokacin da mayakan ISWAP suka yi musu kwanton-bauna.

An ce mayakan sun fito daga Sabil Huda na Sambisa/Bama, suka shigo yankin Timbouctou–Farouq Triangle domin kai harin.

A yayin arangamar, mambobin CJTF biyu – Konto Alhaji da Garba Mohammed – sun rasa rayukansu.

Shugaban sojan kasan Najeriya
Shugaban sojojin kasan Najeriya a bakin aiki. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Rundunar sojin Najeriya ta wallafa a Facebook cewa babu wani jami’in soja da aka tabbatar ya ɓata ko aka sace, sabanin yadda rahotanni marasa tushe suka bayyana.

Kara karanta wannan

Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja

Majiyoyi sun tabbatar cewa duk da tsanantar harin, sojoji sun mayar da martani, suka tarwatsa 'yan ta'addan, sannan suka kare rayukan dakarunsu.

Ba a sace Janar din soja a Borno ba

Bayan arangamar, ɗan ƙaramin ruɗani ya biyo baya, wanda ya sa aka fara yadawa cewa wasu sojoji har da Birgediya Janar sun ɓace.

Amma daga baya yawancin waɗanda aka ce ba a san inda suke ba sun koma sansaninsu cikin koshin lafiya.

Birgediya Janar M. Uba ya fitar da bidiyo domin kawar da jita-jitar, inda ya bayyana cewa:

“Ina raye, lafiya, kuma ina kan jagorancin rundunarmu. Ba wani lokaci da na faɗa hannun ’yan ta’adda.”

Wannan bayanin ya rusa duk wani ikirari na cewa ISWAP ta sace babban kwamandan runduna — wanda a tarihi, da hakan ta faru, da ya kasance karo na farko a Najeriya.

Duk da cewa harin ya faru, gaskiyar ita ce:

– An yi kwanton-bauna, amma ba cikin dare ba

– Mambobin CJTF biyu sun rasa rayukansu.

– Sojoji, ciki har da kwamandan su sun tsira

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

– ’Yan ta’adda sun gudu da wasu babura

Sojoji sun je wuraren ibada a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu dakarun sojin Najeriya sun ziyarci wuraren ibada a jihar Filato domin neman hadin kai.

Yayin da suka ziyarci coci da masallaci, sun bukaci jama'a su rika sanar da hukuma duk abin da ya faru a fadin jihar.

Sun kuma tabbatar da cewa sojoji suna aiki ne domin kare rayukan al'umma ba tare da lura da addini ko kabilarsu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng