Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Ta'addan ISWAP Kwanton Bauna, an Rage Mugun Iri
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun yi nasarar ragargazar 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan ISWAP kwanton bauna lokacin da suke tafiya zuwa dutsen Mandara a yankin Banki na jihar Borno
- Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka daya daga cikin 'yan ta'addan tare da kwato makamai da babura daga hannun tsagerun
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar tarwatsa mayakan ISWAP a jihar Borno.
Sojojin sun tarwatsa 'yan ta'addan ne a wani kwanton-bauna da suka yi musu a yankin Banki na jihar Borno, inda suka kashe ɗan ta’adda ɗaya tare da kwato makamai da babura.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP
Majiyoyi sun tabbatar da cewa farmakin ya gudana ne tsakanin daren ranar 13 ga Nuwamba zuwa safiyar ranar 14 ga Nuwamban 2025.
Hakazalika majiyoyin tsaro sun bayyana cewa kwanton baunar ya ritsa da maharan ne yayin da suke tafiya kan babura dauke da makamai iri-iri daga Bula-Daloye suna kokarin shiga Dutsen Mandara.
Dakarun sojojin sun yi musayar wuta wanda hakan ya tilasta ‘yan ta’addan gudu cikin ruɗani.
“A lokacin bincike a yankin, sojoji sun gano gawar ɗan ta’adda ɗaya, bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, jigidar AK-47 guda biyu, da babura biyu."
- Wata majiya
'Yan ta'addan ISWAP sun tsere
Wasu daga cikin mayakan na ISWAP sun tsere da raunukan harbin bindiga, kodayake ba a iya tantance adadinsu ba.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa babu asara a ɓangaren sojojin, babu kuma wani kayan aiki da aka rasa yayin aikin.
Aikin ya kasance wani ɓangare na ci gaba da yunkurin rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai na kawo karshen ‘yancin zirga-zirgar ‘yan ta’adda da kuma rage karfin su a yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda sun ga ta kansu: Hafsan sojojin sama ya sha alwashi kan rashin tsaro

Source: Original
Karanta wasu karin labaran kan sojoji
- Ko me ya yi zafi: Sojoji sun budewa 'yan sandan da ke dawowa daga zaben Anambra wuta
- Falana: Babban lauya ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan batun juyin mulki
- Wike ya yi magana a fusace bayan sojoji sun fatattake shi a Abuja
- 'Yan ta'adda sun ga ta kansu: Hafsan sojojin sama ya sha alwashi kan rashin tsaro
- Dubu ta cika, sojojin Najeriya sun kama mai sayar wa ƴan ta'adda makamai a Taraba
Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Dakarun sojojin, sun kuma kaddamar da hare-hare kan sansanin Boko Haram/ISWAP da ke wani yanki a jihar Borno, inda suka samu nasarar lalata shi gaba daya.
Hakazalika, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa a yankin Buratai–Kamuya na jihar Borno.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng