An Bindige Matashi a Wajen Jana'izar Mahaifinsa bayan Turnukewa da Harbe Harbe

An Bindige Matashi a Wajen Jana'izar Mahaifinsa bayan Turnukewa da Harbe Harbe

  • An shiga jimami mutuwar tsohon shugaban SUG na Peace Poly, Samuel Udo, bayan harbe shi yayin jana’izar mahaifinsa
  • Rikicin kungiyoyin asiri ya yi sanadin mutuwarsa tare da jikkatar wasu, ciki har da wata budurwa, Choice Ikenger mai shekaru 29
  • Iyalan marigayin da mazauna yankin sun bayyana tashin hankalin da suka shiga, yayin da lamarin ya ƙara tayar da hankalin jama’a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Cross River - Wani mummunan hari ya girgiza al’ummar Ekori a jihar Cross River, inda tsohon shugaban dalibai na Peace Poly, Samuel Sampson Udo, ya rasa rayuwarsa.

An harbe Samuel Sampson Udo ne yayin jana’izar mahaifinsa, lokacin da rikicin kungiyoyin asiri ya turnuke wajen.

Cross River da ke Kudancin Najeriya
Taswirar jihar Cross River a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Leadership ta wallafa cewa taron jana’izar wanda ya kasance na bankwana ga mamacin ya rikide ya zama tashin hankali, bayan fara harba bindigogi.

Kara karanta wannan

Rawar da Bola Tinubu ya taka a rikicin Wike da soja, A.M Yerima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin ya barke a tsakanin kungiyoyin asiri biyu da ke arangama da juna, inda Samuel ya faɗa cikin harbe-harben yayin da yake ƙoƙarin neman mafaka daga wurin.

Yadda aka harbe matashi wajen jana'iza

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ranar 31, Oktoba, 2025, lokacin da kungiyoyin asiri suka yi arangama.

Wani mazaunin yankin, Utum Ofem Ubi, ya ce:

“Ana cikin waƙe-waƙe ne sai kwatsam harbe-harbe suka tashi. Mutane suka fara gudu suna rufe ƙofofinsu.”

A faɗar iyalan mamacin, harin ya faru ne cikin tsananin ta’addanci. ’Yar’uwarsa, Affiong Sampson, ta ce:

“Sun harbe shi kamar dabba. Jikinsa har yanzu yana gidan ajiye gawa, kuma muna cikin baƙin ciki tun ranar da aka kashe shi.”

Wata da ta jikkata a harin, Choice Ikenger, na kwance a asibiti inda har yanzu wani karfen harsasai ke jikinta.

Mahaifiyarta, Silvia, ta ce:

Kara karanta wannan

Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja

“’Yata tana cikin radadi sosai. Mun sha wahala wajen neman ta farfaɗo daga wannan mummunan hari.”

Rikicin kungiyoyin asiri a Cross River

Rikice-rikicen kungiyoyin asiri sun zama ruwan dare a Cross River. A cikin shekarar 2025 kadai, akalla mutane tara aka kashe a lokuta daban-daban.

A watan Afrilu na shekarar nan, rikici a Camp 2 Mfamosing ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, yayin da wasu biyu kuma suka rasa rayuwa a Ikom sakamakon rikicin Vikings da KK.

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode yana jawabi. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Masu lura da al’amura, ciki har da Okoi Obono-Obla, sun sha gargadi kan irin yadda kungiyoyin asiri ke samun ƙarfafawa tare da alaƙa da wasu jami’an kananan hukumomi a yankin Yakurr.

A cewar rahotanni, ana dasa wa matasa da dama akidu marasa kyau, inda ake tilasta musu shiga tsauraran al’adu, cin zarafi, har ma da kashe mutane a matsayin gwajin “ƙarfi”.

An yi rikicin manoma da makiyaya a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa wani rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya faru ne a karamar hukumar Funakaye bayan zargin manoma sun shiga wata gona.

Biyo bayan lamarin, gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da sarakunan gargajiya a yankin bisa gaza hana rikicin faruwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng