Sojoji Sun kai Ziyarar Gargadi da Fadakarwa Masallaci da Coci a Filato
- Janar Folusho Oyinlola ya kai ziyarce-ziyarcen gargadi da faɗakarwa zuwa wuraren ibada na Musulmi da Kirista a Barkin Ladi
- Ya jaddada cewa rundunar sojin Najeriya ba ta goyon bayan ɓangare guda, tana aiki ne don kare kowa ba tare da nuna bambanci ba
- Oyinlola ya ce lokaci ya yi da al’umma za su guji ɗaukar doka a hannu, su rika dakile matsaloli da kafin su rikide zuwa tashin hankali
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – A wani gagarumin yunkuri na ƙarfafa zaman lafiya da kauce wa tashin hankali kafin lokacin girbi da bukukuwan ƙarshen shekara sojoji sun je wuraren ibada a Filato.
Hafsan rundunar sojoji kuma kwamandan OPEP, Manjo Janar Folusho Oyinlola, ya gudanar da jerin ziyarce-ziyarcen sulhu da faɗakarwa a ƙaramar hukumar Barkin Ladi na jihar Plateau.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da kwamandan sojojin ya yi ne a wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shiri na cikin matakan da rundunar sojin Najeriya ke ci gaba da ɗauka cikin lumana domin magance rikicin makiyaya da manoma da ya daɗe yana ci gaba da tayar da hankali a yankin.
'Sojin Najeriya na kare kowa' – Oyinlola
A ziyarar da ya kai wa wani coci a ranar 9, Nuwamba, 2025, Oyinlola ya jaddada matsayin rundunar soji a matsayin mai kare rayuka da dukiyoyi ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
A cikin jawabinsa, Oyinlola ya ce:
“Rundunar sojin Najeriya, rundunar sojin ruwa, rundunar sojin sama da ’yan sanda, duk masu tsare ku ne.
"An kafa su domin amfaninku. Mun kasance a nan dominku, kuma mu wani ɓangare ne na al’ummarku.”
Ya ce rundunar za ta ci gaba da kai dauki cikin gaggawa idan an samu barazana, musamman a yankunan da ke fama da tada ƙayar baya.
Ya ƙara da cewa:
“Ba za mu iya kasancewa a ko’ina ba. Idan kun ga wani abu, ku sanar. Za mu amsa ba tare da ɓata lokaci ba.”
Sojoji sun kai ziyara masallacin Jumu’a
A ranar 14, Nuwamba, 2025, Manjo Janar Oyinlola ya ci gaba da wannan yunkuri, inda ya halarci masallacin Jumu’a a Mahanga domin tattaunawa da al’ummar Musulmai.
Ya bayyana cewa Plateau ta shafe fiye da shekaru 20 tana fama da rikice-rikice da ke haifar da salwantar rayuka, ciki har da jami’an tsaro.

Source: Facebook
Ya ce rikice-rikicen manoma da makiyaya ne tushen mafi yawan matsalolin, yana mai tunatar da yadda dattawa ke sasanta irin wadannan matsaloli ta hanyar tattaunawa maimakon tashin hankali.
Oyinlola ya nuna damuwa cewa yanzu “masu yada rikici” na amfani da bambance-bambance domin cimma manufofinsu ta hanyar tada fitina da tsanantar rikici.
Sojoji sun hana daukar doka a hannu
Kwamandan ya yi kira ga al’umma da su guji daukar matakan da ba su kan doka idan aka samu wata matsala a jihar
“Idan kuna da matsala, kuna da ’yancin zuwa wurin soja. An horar da mu don magance matsalolinku. Kada ku ɗauki doka a hannunku,”
Inji shi.
Ya umurci al’umma da su kasance masu faɗakarwa musamman a lokacin girbi, ganin cewa wannan lokaci yakan ƙara tayar da hankula.
Ya kara da cewa:
“Ina so daga yau kar a ji labarin kisa daga kowanne ɓangare. Idan wani abu ya faru, ku sanar da mu nan da nan,”
Sojoji sun gana da gwamna Umaru Bago
A wani labarin, kun ji cewa kwamandan Operation Fansan Yamma ya kai ziyara jihar Neja domin tattauna matsalar tsaro.
Gwamnan Neja, Umaru Bago ya yaba da kokarin da sojojin suke wajen yaki da 'yan ta'adda a jihar da kasa baki daya.
Umaru Bago ya nemi gwamnatin tarayya ta amince da daukar 'yan jihar N25,000 aikin soja domin su shiga yaki da 'yan ta'adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


