Rawar da Bola Tinubu Ya Taka a Rikicin Wike da Soja, A.M Yerima

Rawar da Bola Tinubu Ya Taka a Rikicin Wike da Soja, A.M Yerima

  • Ana cigaba da magana kan takaddamar da ta barke tsakanin Ministan FCT, Nyesom Wike, sojan Najeriya, A.M. Yerima Abuja
  • Fadar shugaban kasa ta shiga tsakani bayan fadaduwar rikicin zuwa ce-ce-ku-ce kan hurumin FCTA da umarnin rundunar soji
  • An bayyana umarnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumomi domin kauce wa rikicin manyan jami’ai a fadin kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Abuja – A ranar Litinin, 11, Nuwamba, 2025, unguwar Gaduwa ta samu kanta a cikin wani yanayi na tashin hankali.

An samu rikici ne bayan ziyarar bazata da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya so kaiwa wajen wani gini da ake yi.

Shugaba Bola Tinubu, Wike da A.M Yerima
Wike yayin husuma da sojan Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Lere Olayinka
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ziyarar ta fara da nufin tantance aikin gini, amma ta rikide zuwa wani yanayi da ya janyo hankalin mazauna unguwar da suka fito a gigice.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya bayyana cewa ya je wurin ne domin duba filin da FCTA ta ware, amma ake zargin an raba shi ga gine-gine ba tare da izini ba.

Ya kara da cewa yana son tallafa wa jami’an FCTA su binciki wajen da sojoji suka hana su shiga domin duba ayyuka.

Wannan lamari ya haddasa rikici tsakanin ministan da sojoji, lamarin da ya dauki hankali, musamman bayan yadda A.M. Yerima ya tsaya daram wajen bin umarnin aikin soja.

Rawar da Tinubu ya taka a rikicin

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha yabo sosai bayan shigarsa cikin lamarin ta hanyar jagorancin bayan fage, yana jan hankalin hukumomi su bi doka ba tare da tada tarzoma ba.

Rahotanni sun nuna cewa shigarsa cikin lamarin ya taimaka wajen kwantar da hankali tsakanin bangarorin biyu.

A ranar Alhamis, an janye motar ruguza gini da mutanen Wike suka kai wajen domin yin rusau kamar yadda Dino Melaye ya wallafa bidiyon a Facebook.

Kara karanta wannan

A.M Yerima: Tsohon jigon APC, Frank ya shawarci Tinubu ya ja kunnen Wike

Dauke motar ya haifar murna a cikin zukatan mazauna Gaduwa, inda suka rika tafi suna murna kan hakan.

Wike da Yerima: Martanin 'yan Najeriya

Rikicin Nyesom Wike da Yerima ya dauki hankali sosai musamman saboda karfin iko da ministan Abujan ke nunawa.

Wasu na ganin Wike ya hadu da daidai da shi yayin da wasu ke ganin abin da sojan ya yi bai dace da doka ba.

Lokacin da Wike ya yi rikici da soja
Nyesom Wike yayin gardama da A.M Yerima a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Wasu tsofaffin sojoji kamar Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritayi) sun gargadi ministan da cewa abin da ya yi barazana ne ga tsaron kasa baki daya.

Buratai ya ce abin da Wike ya yi tamkar raina shugaban kasa ne da kuma raina dakarun sojojin Najeriya da ke aiki domin kare kasa.

Wike ya yi wa Buratai martani

A wani labarin, kun ji cewa, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi martani kan maganar da tsohon shugaban sojojin kasa, Tukur Buratai ya yi.

Wilke ya ce Buratai bai kai ya koya masa ladabi ba da har zai yi magana a kan abin da ya faru tsakaninsa da wani soja a Abuja.

Kara karanta wannan

'Ka nemi kashe ni,' Wike ya yi martani mai zafi ga Buratai bayan rigima da soja

Ministan Abuja ya yi ikirarin cewa Buratai ya taba sanya wa a kashe shi a lokacin zaben 2019 da Wike ke neman mulki a jihar Rivers.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng