Gwamna Abba Ya Kafa Tarihi, Zai Gabatar da Kasafin Kudin da ba a Taba Kamarsa ba a Jihohin Arewa

Gwamna Abba Ya Kafa Tarihi, Zai Gabatar da Kasafin Kudin da ba a Taba Kamarsa ba a Jihohin Arewa

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin gabatar da kasafin kudin da zai lakume akalla Naira tiriliyan daya a 2026
  • Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a
  • Gwamna Abba ya ce kasafin kudin, wanda zai gabatar a makon gobe, zai zama irinsa na farko a kaf jihohin Arewacin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa gwamnatinsa na dab da kammala aiki kan kasafin kudi na farko da zai lakume akalla Naira tiriliyan 1.

Gwamna Abba ya tabbatar da cewa da zaran an kammala tsara kasafin kudin na shekarar 2026, zai gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano na cikin alheri, Gwamna Abba ya sanya hannu kan dokar kafa sabuwar kwaleji

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano na shirin kasafin kudin N1trn

Gwamnan ya bayyana adadin kudin da kasafin 2026 zai lakume a wurin bude taro na musamman na majalisar zartarwar jihar Kano karo na biyu.

Rahoto ya nuna cewa an kira taron ne domin tattauna shirin kasafin kuɗi na 2026 kafin a mika shi gaban Majalisar Dokokin Kano a mako mai zuwa.

Abba ya ce kasafin kuɗin mai cike tarihi zai kara nuna jajircewar gwamnatinsa wajen inganta manyan ayyukan more rayuwa, gyaran birane da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a fadin jihar.

Yadda Kano ta samu karin kudin shiga

A cewarsa, an samu karin kudin kasafin ne sakamakon bunkasa hanyoyin tara kudaden shiga na cikin gida da kuma rufe duk wata hanyar ɓarnar kuɗaɗe a tsarin tara haraji.

“Mun inganta hanyoyin tara kudaden cikin gida kuma mun rufe kofofin ɓarna, lamarin da ya ba mu damar tsara manyan ayyukan ci gaba a shekarar 2026.”

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya tura 'yan Kano 350 karatu India, ya musu wasiyya mai ratsa zuciya

Gwamnan ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2026 zai fi mayar da hankali kan gina gidaje, noma, ilimi, kiwon lafiya da tallafawa kananan da matsakaitan masana’antu.

Abba Kabir Yusuf ya ce da zarar an kammala, za a tura daftarin kasafin kudin zuwa Majalisar Dokoki don yin nazari da amincewa.

Gwamna Abba.
Hoton kakakin majalisar dokokin Kano, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba zai kafa tarihi a Arewa

Gwamnan ya kara jaddada kudirinsa na bin tafarkin gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa kowane bangare na gwamnati ya samu isasshen kasafi don inganta ayyukan da ake yi wa jama’a.

Ya ce idan Majalisar Dokoki ta amince da shi, wannan zai kasance kasafin kuɗi mafi girma da kowace jihar Arewa ta taɓa gabatarwa.

Gwamna Abba ya kafa kwalejin fasaha

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar kafa kwalejin Gaya domin fadada ilimi da bunkasa fasaha a Kano.

Gwamna Abba ya ce kafa kwalejin Gaya wani muhimmin ginshiki ne a burin gwamnatin sa na farfado da ilimi a matakai daban-daban.

Gwamnan ya yaba wa majalisar dokoki bisa saurin tabbatar da kudirin, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar su wajen kara inganta ilimi a Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262