'Fetur Zai Rage Kudi': IPMAN Ta Fadi yadda Dangote Zai Sauƙaƙa wa ‘Yan Najeriya
- IPMAN ta ce samun man fetur kai tsaye daga Dangote zai rage farashi, sannan zai sauƙaƙa sufuri ga ‘yan kasuwa
- Shugaban IPMAN, Abubakar Shettima ya ce fetur zai yi araha a gidajen mai nan gaba kadan domin wannan sabon tsarin
- Kungiyar ta yi kira ga gwamnati ta biya 'ya'yanta bashin da suka biyo PEF, yayin da ta ce tana da matsala da NMDPRA
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar ’yan kasuwar man fetur ta Najeriya, IPMAN, ta ce sayen man fetur kai tsaye daga matatar Dangote zai taimaka matuka wajen rage farashin mai.
IPMAN ta bayyana cewa, sayen mai daga matatar Dangote, zai sanya gidajen mai su sauke nasu farashin, kuma zai kawo sauƙi ga ‘yan kasuwa da 'yan kasa.

Source: Getty Images
Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Shettima, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a hedikwatar kungiyar da ke Abuja a ranar Alhamis, in ji rahoton The Sun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amfanin sayen fetur kai tsaye daga Dangote
Shettima ya bayyana cewa goyon bayan IPMAN ga gidan mai na Dangote tamkar goyon bayan wani muhimmin ginshiƙi ne na tattalin arzikin kasa.
Ya yi nuni da cewa, matatar man Dangote ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa da tashin farashin mai a Najeriya.
Shugaban ya bayyana cewa samun mai kai tsaye daga Dangote zai kawar da dillalan tsaka-tsaki, abin da ke haifar da karin farashi, musamman a lokutan da ake fama da tsadar sufuri da karancin man.
“Idan aka ba mu mai kai tsaye daga Dangote, babu shakka farashi zai ragu a ko’ina,” in ji Shettima.
Ya ce wannan tsarin zai kuma inganta rabon mai a yankunan da ke da nisa da tashoshin jiragen ruwa, inda akai-akai ake fama da karancin mai da karin kudin sufuri.
An yabi Tinubu, NMDPRA ta sha suka
A yayin taron, Shettima ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa matakin cire tallafin mai, yana mai cewa sabon tsarin ya bude kofar zuba jari iri-iri a bangaren makamashi.
Ya kuma gode wa kamfanin NNPCL, karkashin jagorancin Engr. Bayo Ojulari, bisa fara biyan bashin da kungiyar ke bi shekaru da suka wuce.
Sai dai, ya ce suna da matsala da hukumar NMDPRA, wacce ta kasa biyan bashin da ta gada daga tsohuwar hukumar PEF.
Ya roki ministan man fetur, Sen. Heineken Lokpobiri, ya sa baki don kauce wa yuwuwar daukar matakan da ba su da dadi daga ‘yan kasuwa.

Source: UGC
Kiran haɗin kai a tsakanin 'yan kasuwar mai
Shettima ya yi kira ga mambobin kungiyar da su manta da sabani, su hada kai domin cin gajiyar sababbin damar kasuwanci da suka bayyana a bangaren mai na kasar.
“Lokaci ya yi da IPMAN za ta zama tsjntsiya madaurinki daya. Sababbin damarmakin da ke gabanmu na bukatar hadin kai don samunsu,” in ji Shettima.
Ya tabbatar da cewa IPMAN za ta ci gaba da mara wa matatar Dangote baya, saboda tana da rawar da za ta taka wajen rage farashi da farfado da tattalin arzikin kasa.
"Litar fetur za ta koma N700" Alhaji Kabir.

Kara karanta wannan
Kasa da awanni 24, kotu ta dakatar da babban taron PDP na kasa saboda Sule Lamido
A zantawar Legit Hausa da wani manajan gidan man Shade da ke Kaduna, Alhaji Mubarak Aliyu, ya shaida mana cewa ana samun saukin fetur a yanzu, ta dalilin matatar Dangote.
Alhaji Mubarak ya ce:
"Idan har matatar man Dangote za ta ci gaba da sauke farashin mai idan an samu saukar shi a duniya, to tabbas litar fetur za ta koma ƙasa da N700.
"Ana ci gaba da samun kasashen da ke hako mai, kasuwar duniya na ganin karuwar danyen mai, sannan kasashe da dama sun koma tace man su, dole farashi ya sauka.
"Sannan kamar yadda IPMAN ta fada, idan har ƴan kasuwa za su samu mai kai tsaye daga matatar, to ka ga an huta da biyan kudin jigila, an huta da biyan kudin masu defo, yanzu a gidajen mai kawai za a rika sauke wa, nan ma farashin zai sauka sosai."
'Yan kasuwa za su daina shigo da fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta rage farashin fetur da ₦49 a kan kowace lita, abin da ya girgiza kasuwar sayar da mai a Najeriya.
'Yan kasuwar mai sun ce wannan mataki zai iya kawo ƙarshen shigo da fetur daga kasashen waje, saboda farashin Dangote ya fi rahusa.
Amma wasu masana sun gargadi gwamnatin tarayya cewa dakatar da shigo da man fetur gaba ɗaya zai iya haifar da karancin mai a kasuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


