An Mika wa Majalisar Dokoki Bukatar Kirkirar Sabuwar Jihar Aba a Najeriya

An Mika wa Majalisar Dokoki Bukatar Kirkirar Sabuwar Jihar Aba a Najeriya

  • Kungiyar Aba State Movement (ASM) ta bukaci majalisar dokoki ta tabbatar da Aba a matsayin jiha ta shida a Kudu maso Gabas
  • Ta ce an dade ana gabatar da bukatar ga majalisar kasa tun daga 1952, tare da cewa Aba ta cika dukkan sharudda a tsarin mulki
  • Shugaban kungiyar ya kara da cewa Ohanaeze Ndigbo ta nuna goyon bayan mayar da Aba zuwa jiha ta shida a yankin a 2015 da 2018

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Aba State Movement (ASM) ta sake bukatar majalisar dokoki ta kasa da ta tabbatar da kafa Aba a matsayin jiha ta shida a yankin Kudu maso Gabas.

Kakakin kungiyar, Theo Nkire, ne ya bayyana hakan a Aba, Jihar Abia, yayin da kungiyar ta bayyana dalilan da suka sa ya kamata a fitar da sabuwar jihar daga cikin Abia.

Kara karanta wannan

Wasanni nawa ya rage wa Najeriya ta shiga gasar cin kofin duniya? Bayanai sun fito

'Yan majalisar wakilai
'Yan majalisar wakilai suna zama a zauren majalisa. Hoto: Abbas Tajudeen
Source: Facebook

The Sun ta rahoto cewa Nkire ya tunatar da cewa an gabatar da bukatar kafa Jihar Aba ga majalisar dokoki tun a shekarar 1982.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a ranar 16, Yuni, 1983, majalisar ta ba da shawarar gudanar da kuri’a ta musamman domin tabbatar da kafa jihar. Sai dai juyin mulkin 31, Disamba, 1983 ya katse wannan aikin.

Ya yi karin bayani cewa tun 2009 zuwa 2010, kungiyar ASM ta ziyarci jihohi 21 domin tattara sa hannun 'yan majalisun jihohi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tsara.

Tarihi da bukatar kafa Jihar Aba

Kakakin ASM ya bayyana cewa bukatar kafa Jihar Aba ta taba kasancewa zabin Ohanaeze Ndigbo sau biyu — a 2015 da 2018.

An yi haka ne a lokacin da kwamitocin da aka kafa suka zabi Aba a matsayin jiha ta shida ga yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce wannan bukata ce tafi dadewa a Najeriya, domin tun 1952 ake neman hakan, tare da gabatar da bukata ga kwamitin Willink a 1957.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi gyaran doka, za a koma koyar da dalibai karatu da yare 1

Shugaba Tinubu a majalisar dokoki
Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Nkire ya ce yankin da ake son kafa Jihar Aba ya kunshi kananan hukumomi tara da ke tattare da tarin jama'a.

Ya ce wasu jihohin da ake da su yanzu an kirkire su da kananan hukumomi uku ko hudu kacal, misali Kebbi, Bayelsa da Ebonyi.

Dalilan ASM kan neman kafa jihar Aba

Nkire ya ce yankin Aba na da karfin tattalin arziki sosai, kuma za ta iya dogaro da kudin cikin gida (IGR).

Ya ce a 1998 kananan hukumomi 17 na Jihar Abia sun samar da Naira biliyan 2, kuma kananan hukumomi tara da ake son kafa Jihar Aba sun bayar da kaso mafi yawa.

Ya ce Aba ta yi suna a harkar kasuwanci, masana’antu, noma, man fetur, gas, ma’adanai, wutar lantarki da babban yawan kwararru.

Ya kara da cewa saboda fasahar gargajiya da masana'antu, an dade ana kiran Aba da “Japan din Afrika”.

Kara karanta wannan

Tinubu: Fasto ya tura sako ga Trump kan kashe kashe da ake a Najeriya

Ana nenam kirkiro jihohi 55 a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa kwamitin majalisar dattawa ya fara zama domin tattauna bukatun gyara kundin mulkin Najeriya.

Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa sun samu bukatun kirkirar jihohi 55 a fadin Najeriya.

A wani taro da suka yi a Legas, Sanata Barau ya bayyana cewa majalisar ta fara zama domin nazari kan bukatun da aka mika musu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng