Gwamna Kirista Ya Rusuna, Ya Roki Musulmi game da Zaben Tinubu a 2027

Gwamna Kirista Ya Rusuna, Ya Roki Musulmi game da Zaben Tinubu a 2027

  • Gwamna Monday Okpebholo ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da marawa Shugaba Bola Tinubu baya
  • Okpebholo ya ce goyon bayansu na da matuƙar muhimmanci ga nasarar sauye-sauyen da gwamnati ke yi
  • Gwamnan ya sake nanata alkawarin kawo Tinubu kan gaba a zaben 2027, ciki har da niyyarsa ta samar da kuri’u miliyan 2.5 daga Edo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya roki a'ummar Musulmi game da sake zaben Bola Tinubu a 2027.

Gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin jihar da su tsaya tsayin daka wajen mara wa Shugaba Bola Tinubu baya.

Gwamna ya roki Musulmi su sake zaben Tinubu
Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Godiya da Gwamna Okpebholo ya yi ga Musulmai

Okpebholo ya yi wannan kira ne yayin wani shiri na musamman mai taken “365 Days in Office Celebration Walimah of His Excellency, Sen. Monday Okpebholo” da aka gudanar a birnin Benin, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

Wannan taron na daga cikin abubuwan da gwamnatin jihar ta shirya domin cika shekara guda da gwamnan ya yi a ofis.

Gwamnan ya gode wa al’ummar Musulmi kan addu’oinsu, biyayyarsu da hadin kai da suka bayar tun lokacin da ya hau mulki, yana mai cewa wannan goyon baya ya kasance ginshiki mai muhimmanci ga nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekara guda.

A cewarsa:

“Mun sha wahala, mun sha kalubale da dama, amma da rahamar Allah muka zo nan da Allah ya ba da iko ga duk wanda ya so.
"Tun farko mun bayyana cewa Edo mallakin kowa ce, ba tare da la’akari da addini ko asalin mutum ba.”

Ya kara da cewa dukkan nade-naden gwamnatinsa suna kan gaskiya ne, da cancanta da iya aiki, ba tare da nuna wariya ba.

Gwamna ya bukaci Musulmi su dage da yi wa Tinubu addu'a
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Source: Twitter

Gwamna ya yi alkawarin hadin kan al'umma

A cewarsa, burinsa shi ne tabbatar da hadin kai da habakar jihar Edo, tare da maida siyasa wani aiki na hidima, ba na son zuciya ko bangaranci ba, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

PDP ta yi watsi da Wike da mutanensa, ta ce 'babu fashi' kan taronta na Oyo

Okpebholo ya ce:

“Bukatar Edo tafi bukatar kowane mutum. Wannan shi ya sa nake kira da a ci gaba da yi wa shugaban kasa addu’a. Nigeria daya ce.”

Ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin mutum mai jarumta, halin kirki da gaskiya, wanda ke kokarin gyara kasa ta hanyar sauye-sauye masu karfi.

Ya ce shugaban kasa ya cancanci addu’o’i da goyon bayan al’umma baki ɗaya.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da Tinubu ya samu babban nasara a 2027 a Edo da alkawarin samar da kuri’u miliyan 2.5 domin shugaban kasa.

Ya kara da cewa zai ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Musulmi, yana sauraron shawarwarinsu tare da inganta dangantakarsa da shugabannin addini da na gargajiya a duk fadin jihar.

A cewarsa:

“Soyayya da hadin kai ne ke hada mu.”

Gwamnan Edo ya koka kan basussuka

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi bikin cika shekara daya a kan madafun ikon jihar da ke yankin Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Rai ya yi halinsa: Fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya a Katsina

Monday Okpebholo ya bayyana cewa ya samu jihar cikin wani mawuyacin hali lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2024.

Hakazalika, Gwamna Okpebholo ya bayyana irin dumbin basussukan da aka tafi aka bar shi da biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.