Tinubu Ya Amince da Sake Nada Buba Marwa Shugaban NDLEA zuwa 2031
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sabunta wa Mohammed Buba Marwa nadin shugabancin hukumar NDLEA na shekaru biyar masu zuwa
- Sabon wa’adin yana nufin Marwa zai ci gaba da jagorantar yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi bayan gagarumin nasarar da aka samu tun 2021
- Bola Tinubu ya ce sake naɗin Marwa ya samo asali ne daga ƙoƙarinsa na dakile yaɗuwar miyagun ƙwayoyi da kare matasan ƙasar nan baki daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (Mai ritaya) a matsayin shugaban hukumar NDLEA a sabon wa’adin shekaru biyar.
Wannan na zuwa ne bayan kammala wa’adinsa na farko da aka fara tun watan Janairu 2021 lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi.

Source: Facebook
Legit ta gano haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a X a yau Juma'a, 14, Nuwamba, 2025
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa sabon wa’adin zai bai wa Marwa damar ci gaba da aikin da ya fara na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma yunkurin magance matsalar shaye-shaye.
Marwa, dan asalin jihar Adamawa, ya yi fice a tsawon shekaru a harkokin soja da diflomasiyya tun kafin shigarsa NDLEA.
Tarihin nadin Buba Marwa da gogewarsa
Marwa ya fara jagorantar NDLEA ne a 2021 bayan ya shafe shekaru uku yana jagorantar Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kawar da Shan Miyagun Ƙwayoyi (PACEDA).
Tun bayan zuwansa NDLEA, ya jagoranci manyan samame da kama mutane sama da 73,000 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kwace ƙwayoyi daban-daban.
A fagen ilimi kuwa, Buba Marwa ya yi karatu a jami’o’in Pittsburgh da Harvard tsakanin 1983 zuwa 1986.
A bangaren aikin soja, ya yi aiki a matsayin dogari ga tsohon kwamandan rundunar sojin Najeriya, Laftanar-Janar Theophilus Danjuma.
Rahotanni sun nuna cewa daga baya ya rike mukaman diflomasiyya a Washington DC da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Dalilan sake naɗa Marwa da Tinubu ya yi
A cewar fadar shugaban ƙasa, sake naɗin Marwa wani mataki ne na nuna kwarin gwiwa a kan irin jajircewarsa wajen magance matsalar miyagun ƙwayoyi.
Sanarwar ta ambaci cewa gwamnatin Tinubu na son ganin ci gaba a wannan yaki da ya zama barazana ga matasa da tsaron ƙasa baki ɗaya.
Shugaba Tinubu ya ce:
“Sabunta nadinka tamkar jefa kuri’ar amincewa ce ga ƙoƙarinka na kawar da barazanar fataucin miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye a ƙasar nan.
"Ina kira gare ka ka ci gaba da bin diddigin masu safarar ƙwayoyi da ke ƙoƙarin lalata al’ummar mu, musamman matasa.”
AA Zaura ya kare shugaba Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano, AA Zaura ya kare shugaba Bola Tinubu daga zargin da ake masa kan sauya sheka.
AA Zaura ya ce zargin da ake cewa shugaban na sayen 'yan adawa da kudi domin shiga APC ba gaskiya ba ne.
Ya bayyana cewa ayyukan raya kasa da shugaban ke yi ne suka jawo 'yan siyasa ke sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


