Gaskiya Ta Fito: Amaechi Ya Fadi Tattaunawarsu da Amurkawa kan ‘Kisan’ Kiristoci
- Rotimi Amaechi ya yi magana kan zargin da ake yi musu cewa sun tattauna da Amurkawa kan zargin kisan Kiristoci
- Amaechi ya ce ba su taɓa yin wata ganawa ta sirri da Amurkawa don karya gwamnatin PDP ba, illa dai tattaunawa kan tabbatar da zaben lafiya
- Tsohon ministan ya zargi ’yan jarida da rage yaki da rashin ingantanccen mulki saboda abin duniya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya bayyana abin da ya faru kan zargin sun tattauna da 'yan Amurka kan zargin kisan Kiristoci.
Amaechi ya ce ya zama dole ya fayyace batun ganawar da aka yi tsakanin wasu jagororin adawa da jami’an Amurka a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Source: Twitter
Kiristoci: Amaechi ya karyata ganawa da Amurkawa
Rahoton Vanguard ya ce Amaechi ya bayyana cewa manufar taron kawai ita ce a matsa lamba domin a gudanar da zabe mai inganci da gaskiya.
An yi zargin cewa wasu manyan ’yan adawa sun roƙi Amurkawa su taimaka wajen tilasta faduwar gwamnatin PDP, suna cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.
Amma Amaechi ya musanta hakan kwata-kwata yayin da yake jawabi a babban taron Editoci da aka yi a Abuja.
A cewarsa:
“Ana ta cewa wai an yi wasu taruka na boye a Amurka. Wannan ba gaskiya ba ne. Babu irin wannan taro sau biyu ko uku.
"Akwai taro guda ɗaya kacal inda Amurkawa suka kira mu, suka ce su ba sa son tashin hankali, kuma su na fatan zaɓe zai gudana cikin lafiya.”

Source: Twitter
Amaechi ya soki yan jarida kan aikinsu
Amaechi ya kuma caccaki aikin jarida na yanzu, yana cewa ba kamar lokacin mulkin soja ba, ’yan jarida yanzu ba sa yaki da rashin mulki yadda ya kamata.
Ya kara da cewa:
“Lokacin soja, ’yan jarida sun tsaya tsayin daka. Amma yanzu wasu suna shiru saboda ‘tukunyar cin gajiyar gwamnati ta faɗaɗa’.
A wancan lokacin tukunyar tana karama, soja kaɗai ke cin moriyarta. Yanzu kowa yana da abin ci shi ya sa ba sa magana.”
Amaechi ya ce matsalar Najeriya ba wai kawai rashin tsaro ba ce, illa rashin samar da hanyar halal ga talakawa domin rayuwa.
Ya ce idan gwamnati ta kasa samar da ingantaccen hanyar samun abin yi, jama’a za su ƙirƙiri hanyar haramtacciya domin dogaro da kai.
Ya ce:
“Dalilin da yasa Najeriya ta zama haka shi ne an hana talakawa damar rayuwa. Idan ka hana mutane sanannen hanyar dogaro da kai, to za su ƙirƙiri ta haram.”
Amaechi ya soki wasu na kusa da Buhari
Kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana damuwa kan maganar gyaran tsarin zabe da kullum ake yi.
Amaechi ya ce wasu cikin gwamnatin Buhari sun hana aiwatar da gyaran zabe da tsohon shugaban kasar ya shirya.
Ya bayyana cewa waɗanda suka hana wannan gyara suna cikin gwamnati yanzu, yana mai cewa al’umma ce kawai za ta iya kawo sauyi.
Asali: Legit.ng

