'Ka Nemi Kashe Ni,' Wike Ya Yi Martani Mai Zafi ga Buratai bayan Rigima da Soja
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce an yi wa takaddamar da ta faru tsakaninsa da wasu sojojin ruwa mummunar fahimta
- Ya karyata cewa hakan barazana ne ga tsaron kasa, yana mai bayyana kalaman Tukur Buratai a matsayin rashin fahimtar lamarin
- Wike ya ce bai yi nadama ba game da matsayarsa, yana nan kan abin da ya ɗauka shi ne daidai, duk da maganganu da ake
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ke fassara abin da ya faru tsakaninsa da wasu jami’an rundunar sojin ruwa.
Wike ya yi cacar baki ne da wasu sojoji a ranar Talata da ta gabata, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin kasa.

Source: Facebook
The Nation ta rahoto cewa Wike ya yi martani ga kalaman tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (ma itaya).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buratai dai ya bayyana abin da ya faru a matsayin barazana ga tsaron kasa, amma Wike ya ce tsohon hafsan bai da ikon koya masa ladabi.
Ministan ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya kuma caccaki jami’in sojan da abin ya shafa, Laftanar A.M. Yerima.
Wike ya yi martani ga Tukur Buratai
A yayin da yake martani ga kalaman Buratai, Wike ya ce tsohon hafsan sojin kasa bai isa ya koya masa ladabi ba.
A cewarsa:
“Na karanta abin da wani tsohon babban hafsan sojin kasa ya rubuta. Ba shi ne zai gaya daidai ba, kuma ba shi ne zai koya min ladabi ba.
"Wannan shi ne mutumin da ya umarci GOC dinsa ya yi maguɗin zabe, zabena na 2019. Bai iya min maguɗi ni ba. bai yi nasara ba.”

Kara karanta wannan
Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja
Ya ci gaba da cewa:
“Ya umurci GOC dinsa ya kashe ni amma ba a iya kashe ni ba. Ya zama wakilin wani ɗan takarar shugaban kasa na APC a zaben fidda gwani. A hakan shi ne yake cewa minista ga abin da zai aikata. Ban taɓa ganin irin wannan ba.”
Yadda Wike ya yi rigima da soja
Wike ya ce jami’in sojan ruwan da lamarin ya shafa ya karɓi umarni ba bisa ka'ida ba game da filin da tsohon babban hafsan sojin ruwa, Awwal Gambo, ya yi ikirarin yana da shi.
Sai dai a hirar da ya yi da AIT, Wike ya ce gwamnatin FCT ta tabbatar cewa ba bisa doka ya mallaki filin ba.

Source: Twitter
Ya ce wannan ya sabawa ka’idojin aikin soja da dokar kasa, don haka bai kamata jami’in sojan ya shiga lamarin ba.
A cewarsa:
“Ya karɓi umarni ba bisa doka ba, abin da ya yi ya sabawa doka kai tsaye.”

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Irabor ya tsoma baki kan rigimar Wike da matashin soja a Abuja
Legit ta tattauna da Maikanti
A tattaunawa da Legit Hausa, wani matashi mai bibiyan lamuran yau da kullum, Muhammad Maikanti ya bayyana ra'ayinsa kan abin da ya faru.
Maikanti ya ce:
"Wike yana nuna cewa yana da karfin fada a ji a Najeriya, wani lokaci yana aiki kamar shi shugaban kasa ne.
"Wannan shi zai saka wasu mutane su ji dadin abin da aka masa. Ko shi ne mai gaskiya mutane za su ji dadin abin da sojan ya masa saboda halinsa."
Gargadin tsofaffin sojoji ga Wike
A wani labarin, kun ji cewa tsofaffin sojojin Najeriya sun yi martani game da rikicin da Wike ya yi da wani soja a Abuja.
Manyan sojoji da suka yi ritaya da suka hada da Janar janar sun ce rigima da soja abu ne mai hadari sosai.
Sun bukaci Nyesom Wike ya ba shugaban Najeriya hakuri tare da jami'in sojan da ya fadawa maganganu marasa dadi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
