Rai Ya Yi Halinsa: Fitaccen Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Katsina

Rai Ya Yi Halinsa: Fitaccen Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina ya nuna alhini kan rasuwar fitaccen basarake a jihar wanda aka tabbatar da cewa ya ba al'umma gudunmawa
  • Dikko Umaru Radda ya ce marigayin Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina ya ba da gudunamwa sosai inda ya tura sakon ta'aziyya
  • Ya bayyana marigayin a matsayin shugaba nagari mai tawali’u, hikima da jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar Kusada tare da kare gadon al’ada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya tura sakon ta'aziyya kan babban rashin basarake da aka yi wanda ya kidima al'ummar jihar.

Gwamnan ya tabbatar da rasuwar Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina kuma Hakimin Kusada cikin bakin ciki da alhini kan rashin da aka yi.

Hakimin Kusada a Katsina ya riga mu gidan gaskiya
Gwamna Radda da marigayi hakimin Kusada. Hoto: @dikko_radda.
Source: Twitter

Radda ya shiga jimami kan rasuwar basarake

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana haka ne a shafinsa na X a daren yau Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji da 'yan sanda sun ba hammata iska a Benue, an ji abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Radda ya ce a madadin gwamnatin Katsina da mutanen jihar, yana miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokansa, masarautun Kusada da Katsina bisa wannan rashi mai girma.

Ya ce Alhaji Nuhu Yashe jagora ne na gargajiya mai tawali’u, cikakken basira, wanda ya yi jajircewa wajen zaman lafiya da cigaba a cikin al’ummar Kusada.

Sanarwar ta ce:

"Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un.
"Cikin bakin ciki na samu labarin rasuwar Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina kuma Hakimin ƙaramar hukumar Kusada.
"A madadin Gwamnati da mutanen jihar Katsina, ina miƙa sakon ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautun Kusada da jihar Katsina bisa wannan babban rashi."
Radda ya tura sakon ta'aziyya kan rasuwar basarake
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Gudunmawar da basaraken ya ba al'umma a Katsina

Gwamna ya ce gudummawar marigayi wajen ci gaban yankinsa da kare al’adun gargajiya ba za su shuɗe ba, domin tarihinsa zai ci gaba da haskakawa.

Ya yi addu’ar Allah Madaukaki ya gafarta masa, ya karɓi rayuwarsa cikin Jannatul Firdaus, ya kuma ba iyalansa da al’ummar garin Kusada haƙurin jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Asalin dalilan da suka sa Gwamna Bala ya kirkiro sababbin masarautu 13 a jihar Bauchi

"Alhaji Nuhu Yashe ya kasance fitaccen bbasaraken gargajiya mai cike da tawali’u, basira da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummar mu. Gudummawarsa ga ci gaban al’umma da kare al’adunmu ba za su gushe ba.
"Muna roƙon Allah Maɗaukaki ya gafarta masa, ya ba shi Jannatul Firdaus, ya kuma ba iyalansa da dukan al’ummar garin Kusada haƙurin jure wannan rashi mai raɗaɗi."

- Cewar sanarwar

Masu majiyoyi sun tabbatar da mana da cewa za a yi sallar marigayin bayan sallar Juma'a a yau a kofar Sarki.

Sarkin Hausawa a Benue ya rasu

Mun ba ku labarin cewa an tabbatar da rasuwar Sarkin Hausawan Makurdi, Alhaji Rayyanu Sangami, bayan gajeriyar rashin lafiya a asibitin ABU a Zaria a jihar Kaduna.

An birne marigayin a birnin Makurdi da ke jihar Benue a ranar Asabar 28 Oktobar 2025 da safe bisa tsarin Musulunci bayan an kawo gawarsa daga Zaria da ke jihar Kaduna.

Kungiyar Izala da 'yan siyasa daga ciki da wajen jihar sun yi ta'aziyya ga iyalan marigayin da al’ummar Hausawa a Benue.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.