An Bukaci Tinubu Ya Tilasta Wike Ya ba Yerima Hakuri bayan Zaginsa da Ya Yi

An Bukaci Tinubu Ya Tilasta Wike Ya ba Yerima Hakuri bayan Zaginsa da Ya Yi

  • Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya tsoma baki game da takaddama tsakanin soja da Ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Falana ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya tilasta wa Wike ya nemi gafara ga sojan ruwa da ya yi cacar baki da shi
  • Ya kuma soki sojan ruwa da ya hana Minista gudanar da aikinsa, yana mai cewa duka bangarorin biyu sun yi kuskure

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shahararren lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bayyana ra'ayinsa bayan cacar baki da Nyesom Wike ya yi da soja.

Falana ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya tilasta wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya nemi gafara ga wani jami’in sojan ruwa, A.M. Yerima.

Falana ya ba Tinubu shawara kan Wike
Lauya Femi Falana da Nyesom Wike da sojan ruwa. Hoto: Femi Falana, SAN, Lere Olayinka.
Source: Twitter

Lauya Falana ya soki Wike kan zagin soja

Kara karanta wannan

Wike ya sake kare kansa bayan arangama da soja, ya fadi yadda yake kallon sojoji

Falana ya yi wannan kira ne a wurin bude shekarar shari’a ta 2025 na tsangayar karatun lauyoyi a Jami’ar Abuja, inda ya bayyana cewa duka bangarorin biyu sun yi kuskure, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Falana ya kara da cewa Wike ya yi sa’a bai gamu da hatsari ba, yana mai cewa wannan rigimar ta nuna yadda hukumomi ke yin doka ta karfi a kasar.

Ya ce ba daidai ba ne Minista ya zagi ɗan ƙasa, yana mai cewa:

“Babu Minista da ke da ikon kiran ɗan Najeriya wawa, hatta shugaban kasa ma ba ya da wannan iko.”

Sai dai ya amince cewa Wike yana da hurumin aiki bisa Sashe na 11 na dokar filaye, amma yadda ya dauki lamarin bai nuna natsuwa da kwarewar shugabanci ba.

Lauyan ya dura kan sojan ruwa

Ya kuma soki jami’in sojan ruwa da ya hana Ministan shiga filin aikin, yana mai cewa aikin da yake yi “bai bisa doka ba ne", cewar The Guardian.

Falana ya ce:

“Sojan ya karya doka domin yana tsare kadarar mutum mai zaman kansa, yana ikirarin yana kan umarnin manya, wanda ya sabawa tsarin soja.

Kara karanta wannan

'Ya yi laifi': Asari Dokubo ya fadi matakin da ya kamaci soja bayan rigima da Wike

“Ko shugaban kasa ba zai iya kiran ɗan ƙasa wawa ba, amma Ministan ma ya wuce gona da iri.”
Femi Falana ya caccaki Wike kan zagin soja
Lauya a Najeriya kuma mai kare hakkin al'umma, Femi Falana. Hoto: Femi Falana SAN.
Source: UGC

Falana ya yaba natsuwar soja

Lauyan ya yaba da yadda jami’in sojan ya nuna nutsuwa duk da yadda aka takura masa, yana mai cewa hakan ya nuna kwarewa da ladabi.

A wani bangare, Falana ya soki shirin gwamnati na dawo da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, daga Turai don ci gaba da zaman kurkuku a Najeriya.

Ya tambayi dalilin da yasa gwamnati ke nuna kulawa ga Ekweremadu kawai, alhali akwai sama da ‘yan Najeriya 200 da ke tsare a kasar Burtaniya.

Wike ya kare kansa bayan rigima da soja

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kare rigimar da ya yi da wani jami’in sojan ruwa kan filin da tsohon hafsan ruwa ke ikirari.

Wike ya ce ba zai zauna a ofis ba yana kallo jami’an gwamnati suna fuskantar cin zarafi ba yayin gudanar da aikinsu na hukuma.

Ya kara da cewa ba ya da matsala da rundunar soji, sai dai yana kare doka daga masu amfani da karfin soja don tauye gaskiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.