ADC Ta Taso Shugaba Tinubu a Gaba kan Sabon Bashin da Zai Kinkimo
- Majalisa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu don ciyo bashin Naira tiriliyan 1.15
- Sai dai, jam'iyyar ADC mai adawa ta caccaki bashin wanda Shugaba Tinubu zai kara runtumowa kasar nan
- Ta nuna cewa shugaban kasan ya yi baki biyu bayan a cikin 'yan kwanakin nan ya ce ba zai ciyo bashin cikin gida ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi tsokaci kan bashin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kara ciyowa.
Jam'iyyar ADC ta caccaki bashin na Naira tiriliyan 1.15 tare da zargin gwamnatin tarayya da rashin tsari mai kyau ta fuskantar kashe kudade.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu wadda aka sanya a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ADC ta ce kan bashin Tinubu?
ADC ta ce duk da ikirarin Shugaba Tinubu cewa Najeriya ta cimma burinta na samun kuɗin shiga daga fannonin da ba na mai ba, kimanin Naira tiriliyan 20.59 zuwa watan Agusta 2025, gwamnatin ta ci gaba da cusa kasar nan cikin karin bashi.
Jam’iyyar ta ce bisa rahotannin da ake da su, bashin kasar na iya kai wa Naira tiriliyan 193 idan aka amince da dukkan bukatun rance na shekarar 2025 da Shugaba Tinubu ya nema.
Hakan a cewar ADC, na nuna cewa gwamnati tana ciyo bashi ba tare da ta kawo sauki ga ‘yan kasa da ke fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki ba.
“Amincewar da majalisar dokoki ta kasa ta yi wa sabon bashin cikin gida na Naira tiriliyan 1.15 da gwamnatin APC ta nema, ta sake bayyana rashin daidaiton manufofi kan tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu."

Kara karanta wannan
Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja
- Bolaji Abdullahi
ADC ta tuna cewa a 'yan watannin baya, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta cimma burinta na samun kudaden shiga, inda ta samu Naira tiriliyan 20.59 a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025.
“Baya ga hakan, gwamnati ta taba alkawarin rage ciyo bashin cikin gida, tana mai cewa karuwar kudaden shiga zai taimaka wajen rage jinginar da makomar kasar nan.”
“Gwamnati da ke ikirarin kafa tarihi wajen tara kudaden shiga bai kamata ta ci gaba da neman rance ba. Gwamnati da ta ce za ta daina ciyo bashin cikin gida, bai kamata ta ci gaba da turo bukatun neman tiriliyoyi ba."
- Bolaji Abdullahi

Source: Twitter
ADC ta soki gwamnatin APC
ADC ta kara da cewa gwamnatin APC ta shiga wani yanayi na rudani kan manufofin tattalin arziki.
"Ba za ka iya cewa kudaden shiga sun karu ba, amma a lokaci guda ka kasance kana neman bashi fiye da kowace gwamnati da ta gabata a tarihin Najeriya.”

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya kara dauko wa Najeriya bashin sama da Naira tiriliyan 1
- Bolaji Abdullahi
Kabir Idria ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai damuwa kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ci gaba da karbo basussuka.
"Abin akwai damuwa yadda gwamnati ke ci gaba da karbo basussuka duk da ikirarin da take yi ta cimma adadin kudaden shigan da ta sa ran samu."
"To idan har hakan gaskiya menene kuma dalilin zuwa a karbo wani bashin. Abin da fahimta gwamnatin ba ta son gayawa 'yan Najeriya gaskiya."
- Kabir Idris
Dan ADC ya yi mafarki kan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani dan jam'iyyar ADC, Hon. Nuhu Abdullahi Sada, ya yi mafarki kan Nasir El-Rufai da Rauf Aregbesola.
Ya bayyana cewa mafarkinsa ya nuna cewa El-Rufa’i zai zama shugaban ƙasa a 2027, yayin da Aregbesola zai kasance mataimakinsa.
Hon. Nuhu Abdullahi Sada Sada ya ce duk lokacin da ya yi mafarki mai kyau, yakan zama gaskiya a zahiri saboda haka abin da ya gani zai iya tabbata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
