Wike Ya Sake Kare Kansa bayan Arangama da Soja, Ya Fadi yadda Yake Kallon Sojoji
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kare rigimar da ya yi da wani jami’in sojan ruwa kan filin da tsohon hafsan ruwa ke ikirari
- Wike ya ce ba zai zauna a ofis ba yana kallo jami’an gwamnati suna fuskantar cin zarafi ba yayin gudanar da aikinsu na hukuma
- Ya kara da cewa ba ya da matsala da rundunar soji, sai dai yana kare doka daga masu amfani da karfin soja don tauye gaskiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana bayan takaddama tsakaninsa da wani soja.
Wike ya kansa kan abin da ya faru da shi da wani jami’in sojan ruwa kan filin da ake rikici kansa a Abuja.

Source: Twitter
Wike ya zargi tsohon hafsan sojojin ruwa

Kara karanta wannan
Malami ya fahimci muhimmin abu game da matashin sojan da ya yi gaba da gaba da Wike
Wike ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai kafin taron majalisar zartarwar Abuja da aka gudanar ranar Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zargi tsohon hafsan sojan ruwa, Awwal Zubairu Gambo, da laifin amfani da jami'an sojoji domin tsare filin da gwamnati ke bincike a kai.
Wike ya ce ba zai zauna yana kallo jami’an gwamnati suna fuskantar hari yayin aikin aiwatar da dokoki ba.
Ya ce:
“Ta yaya zan zauna a ofis ina kallo jami’an gwamnati suna shan duka, musamman wadanda ke matakin darakta?”
Ya ce rikicinsa ba da rundunar soji ba ne, sai dai da wani mutum mai zaman kansa da ke amfani da sojoji don aikata laifi.

Source: Facebook
Wike ya caccaki soja ruwa, Yerima
Wike ya caccaki jami’in sojan ruwa, A.M. Yerima, bisa cin zarafin ‘yan sanda da kiransu mummunan suna a wurin aikin da suka je dakatarwa, cewar Daily Post.
Ya ce manyan mutane kamar Obasanjo da Janar T.Y. Danjuma ba sa tura soja, sai dai suna kiran minista don a warware matsalar fili.
"Ina girmama rundunar soja, kuma zan ci gaba da girmama su. Na san abin da wannan hukuma take tsayawa a kai. Ba wawa ba ne ni; na je makaranta.

Kara karanta wannan
'Ya yi laifi': Asari Dokubo ya fadi matakin da ya kamaci soja bayan rigima da Wike
"Don haka duk wanda yake son ya nuna cewa ina da matsala da su, ba daidai ba ne. Ba ni da wata matsala da sojoji, kuma ba zan taɓa yi ba. Me yasa zan sami matsala da gwamnati? Amma wannan lamari na kashin kai ne."
- Cewar Wike
Har ila yau, ministan ya jaddada biyayya ga doka da tsarin gwamnati domin tabbatar da ka'ida a aiki.
Yerima: Yan APC sun taso Wike a gaba
An ji cewa jigon jam’iyyar APC, Joe Igbokwe, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike bayan wani jami’in soja ya yi takaddama da Ministan Abuja, Nyesom.
Wike Igbokwe ya zargi wasu gungun mutane masu kwace filaye da mamaye babban birnin tarayya Abuja, da cin moriyar barnar tsarin gine-gine.
Ya kuma tambayi asalin filin da ake cece-kuce a kai, yana bukatar a bayyana wanda ya mallake shi da yadda aka same shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng