Kwana Ya Kare: Jarumin Fim a Najeriya, Baba Gebu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood ta shiga jimami bisa rasuwar fitaccen dan wasan kwaikwayo, Prince Oyewole Olowomojuore
- Jarumin, wanda aka fi sani da Baba Gebu ya mutu ne a jiya Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025 bayan fama da jinyar wata cuta da ba a bayyana ba
- Jarumin Nollywood, Kunle Afod ya bayyana marigayin a matsayin gwarzo, wanda ya bar tarihin da za a jima ba a manta ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigera - Fitaccen ɗan wasan kwaikwayo a Najeriya kuma jarumi a masana'antar Nollywood, Prince Oyewole Olowomojuore, ya riga mu gidan gaskiya.
Jarumin masana'antar shirya fina-finai da ke Kudancin Najeriya, wanda aka fi sani da Baba Gebu, ya rasu bayan fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Source: Twitter
Wannan labari mai taɓa zuciya ya fito ne daga abokin aikinsa kuma ɗan wasan kwaikwayo, Kunle Afod, wanda ya tabbatar da rasuwar Baba Gebu a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan
Laftanal Yerima: Abin da muka sani game da sojan ruwa da ya fatattaki Wike a Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da rasuwar Jarumi Baba Gebu
Ya wallafa sanarwar rasuwar tare da wasu hotunan marigayin da yammacin jiya Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025.
Wannan rasuwa dai ta girgiza masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood tare da jefa jarumai da abokan arziki cikin jimami da alhini.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Baba Gebu, wanda ya shahara a cikin fina-finan Yaruba, ya rasu ne a ranar Laraba, 12 ga Nuwamba, 2025.
Jarumi Kunle Afod ya bayyana marigayin a matsayin “fitaccen gwarzo” da “ɗan wasa mai bai wa wanda ya bar babban tarihin da za a dade ana tuna wa a masana’antar fina-finai."
Kunle Afod ya rubuta cewa:
“Zuciyata na cikin baƙin ciki yayin da nake sanar da rasuwar gwarzon mu, babban jarumi da ya yi fice, wanda ya rasu da yamma bayan yar gajeruwar rashin lafiya.
"Baba Gebu Allah Ya jikanka, ka huta lafiya, za mu jewarka matuka a masana'antar shirya fina-finai."

Kara karanta wannan
Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya bai wa A.M Yerima kariya bayan takaddama da Wike
Baba Gebu ya kafa tarihi a Nollywood
Bayanai sun nuna cewa marigayi Baba Gebu ya yi fice a masana’antar fim tsawon shekaru masu yawa, inda ya fito a cikin fina-finai da dama da suka shahara.
Mutuwarsa ta jefa masana'antar Nollywood ciki tsananin jimami musamman a tsakanin abokan aikinsa, masoyansa, da masu sha’awar fina-finan da yake fitowa, waɗanda ke alhinin rashi babban jarumi wanda ya bar tarihi.
Tuni dai jarumai, masoya da nasu fatan alheri suka fara tururuwar tura sakon ta'aziyya ga iyalan Baba Gebu, tare da addu'ar Allah ba su hakurin jure rashinsa.

Source: Instagram
Jarumin fim, Duro Michael ya mutu
A wani rahoton, kun ji cewa jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta Kudancin Najeriya watau Nollywood, Duro Michael ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun nuna cewa Jarumi Michael ya mutu yana da shekaru 67 da haihuwa bayan fama da doguwar rashin lafiya.
An bayyana cewa marigayin ya dade yana kwance ba shi da lafiya, amma bai samu tallafi daga abokan sana'arsa na masana'antar Nollywood ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng