Fasinjoji na Tsaka Mai Wuya da Jirgin Kasa Ya Sake Samun Matsala a Hanyar Abuja
- Jirgin kasan da ke jigilar fasinjoji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya gamu da matsala yayin da yake tsaka da tafiya
- Lamarin dai ya auku ne bayan jirgin wanda ke dauke da fasinjoji ya fara tafiya daga Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja
- Wani fasinja da ke cikin jirgin ya bayyana cewa ba a yi musu bayanin abin da ke faruwa ba, illa dai kawai sun ga jirgin kasa ya juya baya suna cikin tafiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Fasinjoji da ke cikin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja sun makale a tsakiyar hanya.
Fasinjojin sun makale ne bayan da jirgin ya samu matsalar da ta tilasta masa dawowa Kaduna bayan tafiya ta kusan awa guda.

Source: UGC
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa jirgin ya tashi daga tashar Kaduna a ranar Alhamis da misalin karfe 2:00 na rana da ‘yan mintuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin kasan Abuja kaduna ya samu matsala
Sai dai, bayan ya yi tafiya ta wani lokaci sai ya samu matsala wanda ya sa ma’aikatan jirgin suka juyar da shi zuwa Kaduna domin gyara.
Wani fasinja daga cikin jirgin wanda bai so a ambaci sunansa ba ya ce ma’aikatan jirgin ba su fadi abin da ke faruwa ba, sai dai kawai suka ga jirgin ya fara juyawa baya ba tare da wani bayani ba.
“Mun ga kamar jirgin ya tsaya na ɗan lokaci, sai daga baya kawai muka lura yana juyawa baya zuwa Kaduna. Kowa ya shiga fargaba."
- Wani fasinja
An tabbatar da aukuwar lamarin
Wani ma’aikacin hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) a Kaduna, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya bayyana cewa jirgin ya tashi a daidai lokacin da aka tsara na karfe 2:00 na rana ne amma ya fuskanci matsala a hanya sannan aka dawo da shi don gyara.
“Yanzu haka, yawancin fasinjojin da ke son zuwa Abuja sun makale a tashar Kaduna suna jiran a gyara jirgin. Wasu kuma sun koma gidajensu saboda rashin tabbas kan lokacin tafiya."
- Wani ma’aikacin NRC
Lamarin ya kara tayar da damuwa tsakanin matafiya da ke amfani da jirgin kasan Abuja–Kaduna.

Source: Original
Karanta wasu karin labaran kan jirgin kasa
- Ta faru ta ƙare: Hukumar jiragen ƙasa ta dakatar da zirga zirga daga Kaduna zuwa Abuja
- "Ku yafe mani," An ji wanda ya 'jawo' hatsarin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja
- NSIB ta gano wasu bayanai kan hatsarin jirgin Kaduna, an ji halin da fasinjoji 6 ke ciki
Jirgin kasa ya murkushe mota
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin kasa ya murkushe wata mota a yankin Iju-Fagba, da ke jihar Legas.
Motar da jirgin kasan ya murkushe wadda aka ce kirar Toyota Sienna ce, na dauke ne da buhunan shinkafa a cikinta lokacin da hadarin ya auku.
Hadarin dai ba shi ba ne irinsa na farko da yake aukuwa a tsakanin motoci da jiragen kasa ba a jihar Legas.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

