'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Kai Harin Ta'addanci a Sokoto, Sun Yi Barna Mai Girma
- 'Yan ta'addan Lakurawa sun kai wani harin ta'addanci a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Tsagerun 'yan ta'addan sun yi dirar mikiya cikin wani kauye inda suka bude wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Harin da 'yan ta'addan suka kai ya jawo sanadiyyar rasa rayuka tare da raunata mutane masu yawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Harin 'yan ta'adda da ake zargin na Lakurawa ne ya sanya tsoro da bakin ciki sun mamaye al’ummar kauyen Alkalije da ke cikin yankin Kilgori a karamar hukumar Yabo ta jihar Sokoto.
Mummunan harin da 'yan ta'addan na Lakurawa suka kai ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyar, ciki har da mata mai dauke da juna biyu.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce mazauna yankin sun ce maharan sun dirar musu da asuba a ranar Litinin, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Lakurawa sun kai hari a Sokoto
Kauyen Alkalije, wanda ke da iyaka da Silame da jihar Kebbi, ya kasance karkarar da aka san ta da zaman lafiya, amma yanzu ya zama fagen tsoro saboda hare-haren da ake dangantawa da kungiyar ‘yan ta'addan Lakurawa.
Wani ganau ya ce waɗanda aka kashe sun mutu nan take yayin harin, yayin da wasu biyu suka samu rauni mai tsanani sakamakon harbin bindiga, kuma yanzu haka suna jinya a wani asibiti da ke kusa.
Alhini ya karu a cikin al’ummar yankin bayan tabbatar da cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu mace ce mai juna biyu, wadda harsashi ya same ta yayin da take kokarin tserewa tare da ‘ya’yanta biyu.
Wani mutum da ya tsira daga harin ya bayyana abin da ya gani da cewa:
“Sun shigo da babura, sama da guda 12. Ba su ce da kowa komai ba, sai kawai suka fara harbi. Mutane suka rika gudu, amma sun bi wasu suka kashe su ba tare da tausayi ba.”

Kara karanta wannan
Ganduje, Barau da wasu kusoahi sun dura majalisa da 'yan majalisar NNPP 2 suka koma APC
Jama'a sun bukaci dauki
Wani jagoran al’umma da ya nemi a ɓoye sunansa ya yi Allah wadai da yawaitar hare-haren, yana mai zargin cewa rashin cibiyar tsaro ta dindindin a yankin shi ne babban dalilin da ya sa ake kawo musu farmaki.
“Waɗannan ‘yan bindiga suna shigowa da fita yadda suka ga dama. Suna ketowa daga jihar Kebbi da wasu sassan Silame suna kai mana hari, su kuma ɓuya cikin daji."
"Suna karɓar haraji daga hannunmu, suna kuma barazana cewa za su dawo idan ba mu biya ba. Rayuwarmu ta koma cikin tsoro kullum.”
- Wani jagoran al'umma

Source: Original
Ya roƙi gwamnatin jiha da ta tarayya su taimaka da gaggawa ta hanyar kafa sansanin sojoji ko ‘yan sanda a yankin don dakile hare-haren.
“Ba za mu ci gaba da binne ‘yan uwammu ba yayin da muke jiran taimako da bai zuwa."
- Wani jagoran al'umma
'Yan bindiga sun sace mata a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun sace wasu mata tara a harin da suka kai kauyen Bargaje, da ke karamar hukumar Isa.
Yan bindigan waɗanda ake zargin yaran Bello Turji ne, sun mamaye kauyen haye a kan babura, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

