‘Ya Yi Laifi’: Asari Dokubo Ya Fadi Matakin da Ya Kamaci Soja bayan Rigima da Wike
- Tsohon jagoran ‘yan tawaye na Niger Delta, Asari Dokubo, ya yi magana kan rigimar da ta kaure tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da jami’an soja
- Asari ya ce sojan da ya yi gardama da Wike ya kamata a hukunta shi, a tsare shi kuma a gurfanar da shi gaban kotun sojoji
- Ya jaddada cewa Wike shi ne babban jami’in tsaro na Abuja, don haka babu soja ko jami’i da ya isa ya kalubalance shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon jagoran ‘yan tawaye na yankin Niger Delta, Alhaji Asari Dokubo, ya yi Allah-wadai da sabanin da ya faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu sojoji.
Dokubo ya bayyana damuwa kan abin da ya faru da wasu jami’an soja da Wike kan filin da ake takaddama a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan
Hadimin Kashim Shettima ya fadi 'mai gaskiya' tsakanin Wike da matashin soja, A.M Yerima

Source: Twitter
Dalilin cacar baki tsakanin Wike da soja
A cikin wani bidiyo da Asari ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce jami’in da ya yi hakan ya kamata a hukunta shi tare da gurfanar da shi a kotun soja.
Hakan ya biyo bayan wani cacar baki tsakanin jami'in soja da Wike yayin da ministan ke kokarin kutsawa cikin filin
Yayin rigimar, jami’in sojan ruwa ya ce yana aiki ne bisa umarnin tsohon shugaban rundunar ruwa, Vice Admiral Awal Gambo, inda ya hana Ministan shiga filin da ake gardama.
Abin da Dokubo ke gani kan lamarin
Wannan lamari ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin Ministan da jami’an sojan, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga al’umma da ‘yan jarida a Abuja.
Sai dai Asari ya bayyana cewa yin mu’amala da Ministan Abuja da rashin mutunci ba abin da ake amincewa da shi ba ne, domin shi ne gwamnan Abuja bisa tsarin doka.

Kara karanta wannan
A.M Yerima da Wike: Jerin mutane 4 da ke da karfin ikon bai wa soja umarni a Najeriya
Ya ce:
“Ba wai ina goyon bayan Wike ba, amma ina goyon bayan doka da tsarin da kasa ta tanada. A kowace kasa mai hankali, da an kama wannan jami’i.
“Ko da ban kaunar Wike, amma wannan lamari abin kunya ne. Ba zai taba faruwa a wata kasa mai tsari ba face a Najeriya.”

Source: Twitter
Wike: Asari Dokubo ya soki Laftanar Yerima
Asari ya kuma tunatar da cewa babu wanda ya isa ya fara aikin gini a Abuja ba tare da bin ka’idojin gwamnati da dokokin cigaba da kadarori ba.
Ya ce jami’an soja kamar sauran ‘yan kasa suna karkashin tsarin mulki, ba su da ikon yin abin da suke so ba tare da bin doka ba.
A cewarsa:
“Wike ya tafi wurin ne saboda aikin gwamnati, domin idan bai je ba, da za a zargi jami’an gwamnati da rashin kulawa da aikinsu.”
Ya kammala da cewa babu wanda zai yarda da irin wannan rashin kunya daga soja ga Minista wanda doka ta tabbatar shi ne babba a birnin tarayya.
Matawalle ya soki Wike kan rigima da soja
Mun ba ku labarin cewa karamin Ministan Abuja, Bello Matawalle ya soki Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa sa’insa da jami’in sojan ruwa.
Ya ce bai dace Wike ya rika cacar baki da ƙaramin jami’i ba bayan akwai shugabanninsa da ya dace ya gana da su.
Bello Matawalle ya jinjina wa A.M Yerima bisa ladabi da biyayya da ya nuna a lokacin da Wike ya ja jama'arsa inda sojojin su ke.
Asali: Legit.ng
