Asalin Dalilan da Suka Sa Gwamna Bala Ya Kirkiro Sababbin Masarautu 13 a Jihar Bauchi

Asalin Dalilan da Suka Sa Gwamna Bala Ya Kirkiro Sababbin Masarautu 13 a Jihar Bauchi

  • Gwamnatin Bauchi ta share tantamar jama'a kan dalilanta na kafa sababbin masarautu 13 tare da nada sarakuna a jihar
  • Sakataren gwamnatin Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo ya ce karuwar jama'a da kauyuka na cikin abubuwan da gwamnati ta dogara da su
  • Ya bayyana cewa mutanen Bauchi sun yi farin ciki da wannan mataki, kuma sun karbi wadanda aka nada a matsayin sarakuna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ta fito ta yi bayani kan dalilanta na kirkiro sababbin masarautu 13.

A kwanakin baya ne, Gwamna Bala ya rattaba hannu kan dokar kafa masarautu 13 a jihar Bauchi, tare da nada sarakuna da hakiman da za su jagoranci al'umma.

Gwamna Bla Mohammed.
Hoton mai girma gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed a gidan gwamnatinsa Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Dalilan kirkiro masarautu 13 a Bauchi

A wani rahoto da Leadership ta wallafa, gwamnatin Bauchi ta ce ta yi haka ne domin ƙara haɓaka ci gaban jama’a da kusantar da mulki ga ƙananan hukumomi da al’umma.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya gana da sojoji, an lalubo hanyar hana 'yan bindiga shiga Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Alhaji Aminu Hammayo, ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a Bauchi.

Ya fadi haka ne jim kaɗan bayan taron kwanaki biyu da Gwamna Bala ya gudanar da sababbin sarakuna 13 da tsofaffi shida

“Dalilin ƙirƙirar sababbin masarautu shi ne domin a kusantar da gwamnati ga jama’a. Mun sha faɗa cewa yawan jama’ar mu ya ƙaru sosai, kuma ayyukan ci gaba ya fara isa har ƙananan yankuna,” in ji shi.

Ya ce wasu tsofaffin masarautun da ake da su a jihar suna da faɗi sosai idan aka kwatanta da wasu jihohi, inda daga ƙarshen wani yankin zuwa wani na iya kaiwa kilomita 200, abin da ke sa gudanar da mulki ya zama mai wahala.

Gwamnatin Bauchi ta faranta ran jama'a

A cewarsa, yawan jama’a ya ƙaru ƙwarai, tare da canje-canjen al’adu da ƙarin ƙauyuka da ke buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Aminu Hammayo, wanda kuma shi ne Magatakardan Misau, ya tuna cewa a lokacin taron:

“Mun gani da idonmu irin farin ciki, murna da shagulgula da jama’a suka nuna saboda ƙirƙirar sababbin masarautu tare da nadin sababbin sarakuna.”
“Sun nuna gamsuwa da nadin da aka yi musu, kuma wannan shi ne karo na farko da suka gana kai tsaye da gwamna.
"Taron ya gudana cikin kwanciyar hankali, kowa ya yi farin ciki, kuma kamar yadda aka fara da kyau, haka ya ƙare da kyau.”
Gwamna Bala Mohammed.
Hoton Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Bauchi na shirin kafa kananan hukumomi 29

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kirkiro sababbin kananan hukumomi 29 a jihar Bauchi domin inganta harkokin mulki.

A wata takarda da ta fito, mukaddashin mataimakin magatakardan Majalisar Dokokin Bauchi, Musa Yerima, ya aika kudurin kafa kananan hukumomin ga Majalisar Tarayya.

A halin yanzu, Jihar Bauchi ta na da kananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin 1999 ya amince da su, idan aka kara 29, sun zama 49 kenan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262