Tinubu Ya Bukaci 'Yan Jarida Su Rika Adalci da Fadin Gaskiya kan Gwamnatinsa

Tinubu Ya Bukaci 'Yan Jarida Su Rika Adalci da Fadin Gaskiya kan Gwamnatinsa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci kafafen yada labarai su rika yin suka da ilimi, adalci don gina kasa ba tare da rusa ta ba
  • Ya ce gwamnati, ’yan kasuwa da kungiyoyin farar hula da kafafen yada labarai suna da rawar da za su taka wajen ci gaban kasa
  • Tinubu ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da inganta tsaro, habaka tattalin arziki da samar da damammaki ga ’yan kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci kafafen yada labarai da ’yan jarida a Najeriya su rika yi wa gwamnatinsa adalci.

Ya bukaci su rika yin suka kan manufofin gwamnati da kyakkyawar niyya, ilimi, da adalci, domin taimakawa wajen gina kasa mai dorewa, ba rushe ta ba.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Dalilin da ya sa Amurka ba za ta saka wa Najeriya takunkumi ba

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Tinubu yayin wani jawabi a jihar Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da shugaban kasar ya yi ne a wani sako da Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran Tinubu ga 'yan jarida masu sukarsa

Bola Tinubu ya ce gina kasa ba wai a kan gyaran tattalin arziki kadai yake ba, yana bukatar hadin kai, amana, da fahimtar cewa makomar Najeriya tana hade da kowa da kowa.

Shugaban kasar ya yaba da taken taron yana mai cewa manufar shi ne a duba yadda tattaunawar jama’a za ta karfafa dimokuraɗiyya ko kuma ta raunana hadin kan kasa.

Tinubu, wanda shi ne shugaban kasa na farko da ya halarci irin wannan taro tun kafa Najeriya, ya jaddada cewa zuwan zamanin kafafen sada zumunta ya sauya tsarin yada labarai.

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban ya koka kan yadda kowane dan kasa ke iya zama mai wallafa labarai a kafafen sadarwa.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu suka bullo wa barazanar harin Amurka sun fara jan hankali

“Wannan na da amfani, amma kuma yana kara yaduwar labaran karya cikin sauri. Karya tana iya karbuwa kafin gaskiya ta samu damar magana.
"Don haka tabbatar da sahihanci ya zama ginshiki, daidaito ya zama ka’ida, da kuma sanin aiki ya zama jagora.”

Tinubu ya kara kira ga 'yan jarida

Shugaba Tinubu ya bukaci editoci su rika bin ingantattun ka’idojin aikin jarida, su rika ba da rahotanni cikin gaskiya da kwarin guiwa, tare da yin suka ga gwamnati da hujja da adalci.

Ya ce:

“Sauye-sauyen da muka aiwatar suna da wahala amma an tsara su ne don gina tattalin arzikinmu bisa tushe mai karfi.
"Mun dauki matakan dawo da daidaiton tattalin arziki, karfafa zuba jari, da dawo da kwarin gwiwa.
"Alamun ci gaba sun fara bayyana, amma har yanzu akwai sauran aiki kafin ’yan Najeriya su ji canjin a rayuwarsu ta yau da kullum.”
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron Editocin Najeriya karo na 21 da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, a ranar Laraba.

Trump: Aso Rock Villa ta kare Tinubu

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi da wasu manyan mutane da Tinubu ya tattauna da su kan barazanar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu yana daukar matakan kan matsalar tsaro.

Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce Tinubu na kokarin warware matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.

Ya kara da cewa yana da tabbas cewa shugaban Amurka, Donald Trump ba zai sanya wa Najeriya takunkumi ba kan zargin kisan Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng