A.M Yerima da Wike: Jerin Mutane 4 da ke da Karfin Ikon Bai Wa Soja Umarni a Najeriya
Abuja, Nigeria - Takaddamar da ta faru tsakanin ministan harkokin Abuja, Nyesom Wile da sojojin ruwa na ci gaba da jan hankalin yan Najeriya.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sai dai ganin yadda matashin sojan ruwa, A.M Yerima ya ki bin umarnin Wike, jama'a sun fara neman sanin abin da doka ta tanada kan wanda zai iya tankwara soja a bakin aiki.

Source: Twitter
Yadda soja ya taka wa Wike burki
A yayin sa-in-sa da Wike, sojan ya nanata cewa yana aiki ne bisa umarnin da manya suka ba shi a gidan soja, don haka babu wanda zai kawo masa tangarda, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya samo asali ne lokacin da Ministan da tawagarsa suka nemi shiga wani fili da ake takaddama a kansa, wanda sojojin ruwa ke tsarewa, amma jami’an suka ƙi bari.
Wani abu da ya kara jan hankali shi ne yadda Laftanal A.M Yerima ya yi kokarin nuna kwarewa tare da kare mutuncinsa duk da kalamai masu daci da aka ji Wike na jifarsa da su.
Jerin masu ikon bai wa soja umarni
Da yake hira da BBC Hausa, wani tsohon jami'in rundunar sojin ruwa da ya kai matsayin Kaftin, Umar Bakori ya bayyana cewa tsarin aikin soja “iri ɗaya ne a duk duniya."
Ya ce wannan tsarin yana tabbatar da cewa duk jami’i dole ne ya yi biyayya ga wanda ke gaba da shi a muƙami, komai ƙarfinsa ko matsayin sa a runduna.
Haka kuma, doka ta fayyace wasu keɓaɓɓun mutane da duk wani soja dole ne ya bi umarninsu, ga su kamar haka:
1. Shugaban kasa
Kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya da dokoki gidan soja suka tanada, Shugaban Ƙasa shi ne Babban Kwamandan Rundunonin Soji na kasa.
Saboda haka, mai girma shugaban kasa ko da farar hula ne, yana da ikon bayar da umarni kai tsaye ga kowanne soja, kuma wajibi ne duk jami’an tsaro su bi wannan umarni a duk inda suke.

Kara karanta wannan
Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja
2. Wanda ke gaba da kai a muƙami
A dokar gidan soja, wandake gaba da kai a mukami yana da ikon da zai ba ka umarni kuma dole ka yi masa biyayya.
Wannan ya sa a bidiyon takaddamar Wike da sojoji, akwai lokacin da jagoran tawagar da ke tsaron filin, A.M Yerima ya rika ba abokan aikinsa umarni ka da su tayar da hatsaniya.
A cewar Umar Bakori, idan babban soja ya ba da umarni dole na kasa da shi su yi biyayya kuma ko da an gano akwai kuskure, sai dai a ba babban sojan shawara ya janye.
3. Ministan tsaro
A wasu lokuta, Ministan Tsaro na iya bayar da umarni kai tsaye ga jami’an sojoji a madadin shugaban kasa kuma dole a masa biyayya bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Dokar gidan soja ta tanadi cewa idan ministan tsaro ya ba da umarni a matsayin wakilin shugaban kasa, dole ne a masa biyayya.

Source: Facebook
4. Muƙaddashin Shugaban Ƙasa

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Irabor ya tsoma baki kan rigimar Wike da matashin soja a Abuja
Mutum na karshe da doka ta ba karfin bai wa sojoji umarni shi ne mukaddashin shugaban kasa, dole ne kowane jami'i ya masa biyayya kamar yadda yake wa shugaban kasa.
Tsohon sojan ruwa, Umar Bakori ya jaddada cewa banda waɗannan mutane, shugaban kasa, wanda ke gaba da kai, ministan tsaro, da muƙaddashin shugaban kasa, babu wanda doka ta ba da izinin sarrafa soja.
Ya ce duk wani umarni da ya fito daga wani da ba ya cikin waɗannan, ba dole ba ne soja ya bi shi, domin hakan zai zama karya tsarin soja da dokar ƙasa.
DHQ ta tada kura bayan rikicin Wike
A wani labarin, kun ji cewa Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta wallafa wani sako wanda ya haddasa ce-ce-ku-ce kan abin da ya faru tsakanin Ministan Abuja da sojoji.
Wasu na ganin kalmomi uku da DHQ ta fitar na nuna goyon baya ga jami'in rundunar sojin, wanda ya taka wa Wike burki a Abuja.
Hedkwatar tsaron kasa ta sake jaddada cewa yin hidima a rundunar sojin Najeriya babban girmamawa ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
