Ana Batun Matashin Soja da Wike,Tinubu Ya Yi Magana kan Jarumtar Sojojin Najeriya
- Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan abin da ya faru tsakanin sojan ruwa, A.M Yerima da Ministan Abuja, Tinubu ya yabawa dakarun sojoji
- Shugaba Tinubu ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya maza da mata sun cancanci yabo bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare kasa
- Bola Tinubu ya amince cewa Najeriya na fama da matsalar ta'addanci amma gwamnatinsa ta shirya tunkarar kowane kalubale
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa dakarun rundunar sojojin Najeriya mazansu da matansu bisa yadda suka bayar da rayuwarsu wajen kare kasa.
Wannan yabo na zuwa ne yayin da ake ta surutu kan matashin sojan ruwa, Laftanal A. M Yerima, wanda ya shafa kwalli a idonsa, ya hana ministan Abuja, Nyesom Wike shiga wani fili.

Kara karanta wannan
Laftanal Yerima: Abin da muka sani game da sojan ruwa da ya fatattaki Wike a Abuja

Source: Twitter
Tinubu ya jinjinawa sojojin Najeriya
Shugaba Tinubu ya ce sojoji sun cancanci yabo domin kara masu kwarin gwiwa duba da irin jajircewa da sadaukarwar da suke yi wajen tsare kasar nan, cewar rahoton Channels tv
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai girma Bola Ahmed ya yabi sojojin ne yayin da yake jawabi a taron ƙungiyar editoci ta Nigerian Guild of Editors (NGE) a Abuja ranar Laraba, 12 ga Nuwamba, 2025.
Shugaba Bola Tinubu ya yi tambayoyi masu muhimmanci game da rawar da sojojin ke takawa wajen kare ƙasar nan dafa duk wani nau'i ma barazana.
Tambayoyin Tinubu ya yi kan aikin sojoji
Ya ce, la’akari da haɗarin da sojojin Najeriya ke fuskanta wajen kare iyakokin Najeriya, dole ne al’umma su nuna goyon baya da ƙarfafawa gare su, in ji Vanguard.
“Eh, muna fuskantar ƙalubale na ta’addanci, ‘yan fashi da sauran matsaloli, mun san haka. Shin muna yin wani abu game da hakan? Shin muna ƙarfafa sojojinmu? Shin muna karfafa musu gwiwa su ci gaba da yaƙi?
"Su na ba da rayuwarsu a fagen fama, wasu su jefa rayukansu cikin haɗari don kare ikon ƙasar nan. Wannan nauyi ne a wuyanmu duka,” in ji Tinubu.
Jawabin shugaban ƙasa Tinubu na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalolin tsaron da suka addabi sassan ƙasar nan, wanda ke jawo asarar rayuka.

Source: Facebook
A ranar Alhamis da ta gabata, Shugaba Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na zurfafa hulɗar ƙasa da ƙasa da ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da aikata miyagun laifuka.
“Aikin da ke gaban mu babba ne. Amma mun ɗaura damarar tunkararsa cikin haɗin kai da ƙuduri, don mu kawar da ta’addanci kuma mu gina Najeriya mai wadata, haɗin kai da ƙarfi,” in ji shi.
Babachir ya soki Tinubu kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Babachir Lawal ya zargi gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen magance matsalolin tsaro a kasar nan.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya yi ikirarin cewa Tinubu ba shi da niyyar magance matsalar tsaro.
Babachir Lawal ya kuma soki mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, yana cewa bai ga wani abin kirki da ya yi a ofishinsa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

