DHQ: Hedkwatar Tsaro Ta Wallafa Kalmomi 3 bayan Soja Ya Fatattaki Ministan Abuja, Wike

DHQ: Hedkwatar Tsaro Ta Wallafa Kalmomi 3 bayan Soja Ya Fatattaki Ministan Abuja, Wike

  • Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta haifar da cece kuce yayin da ta wallafa wani sako bayan rikicin ministan Abuja da sojan ruwa
  • Wasu na ganin kalmomi uku da DHQ ta fitar na nuna goyon baya ga jami'in rundunar sojin, wanda ya taka wa Wike burki a Abuja
  • Ministan Abuja, Neysom Wike ya gamu da tangarda yayin da wasu sojojin ruwa suka hana shi shiga wani fili da ake aikinsa a Abuja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta wallafa wani takaitaccen sako wanda ya haddasa ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta saboda abin da ya faru tsakanin Ministan Abuja da sojoji.

Wasu na ganin cewa sakon wanda ya kunshi kalmomi uku da rundunar sojojin Najeriya ke amfani da su, alama ce ta goyon bayan sojan da ya yi sa-in-sa da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya bai wa A.M Yerima kariya bayan takaddama da Wike

Nyesom Wike da A.M Yerima.
Hoton ministan Abuja, Nyesom Wike da na jami'in rundunar sojin ruwa, A. M Yerima
Source: Twitter

A sakon da ta wallafa a shafin X da yammacin ranar Talata, hedkwatar tsaron kasa ta sake jaddada cewa yin hidima a rundunar sojin Najeriya babban girmamawa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalmomi 3 da hedkwatar tsaro ta wallafa

Ta kuma jero kalmomi uku masu karfi: “Ba a girgiza mu. Ba a lankwasa mu. Ba a karya mu," lamarin da wasu suka fassara da goyon bayan jami'in da ya hana Wike shiga fili a Abuja.

DHQ ta wallafa wannan saƙo ne jim kadan bayan takaddama mai zafi tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojin ruwa, Laftanal A.M. Yerima, a wani fili a Abuja.

Hedkwatar tsaro ta ce:

"Aiki a rundunar sojin Najeriya girmamawa ne. Ba a girgiza mu. Ba a lankwasa mu. Ba a karya mu."

Mutane sun maida martani ga DHQ

Sai dai wannan saƙon, wanda ba a fayyace ma’anarsa ba, ya haddasa ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Hana Wike shiga fili a Abuja, Lauya ya fadi zunubin da sojan ruwa ya aikata

Wasu daga cikin masu amfani da kafafen sun fassara shi a matsayin goyon baya ga matashin sojan ruwa, A. M Yarima wanda ya yi takaddama da Wike.

Wani mai suna, @Kwara_Yakoyo, ya yi zargin cewa DHQ ta yi kamar tana goyon bayan “ayyukan da suka sabawa doka,” yana cewa:

“Wannan kamar yabo ne ga jami’in da ya hana wakilin gwamnati gudanar da aikinsa na doka. Lallai muna da matsala a wannan ƙasa.”

Wani mai amfani da X, @MeneFreeman, ya rubuta cewa ya yabawa matashin sojan yana mai cewa Yerima “ya yi daidai.

“Idan babban hafsan tsaro na kasa watau CDS ya amince da bayaninsa, hakan na nuna cewa jami’in ya yi abin da ya dace,” in ji shi.

@FemiBadekale kuma ya kara da cewa:

"Lt. Yerima ya wakilci sojojin Najeriya da ƙwarewa da mutunci. Ya cancanci karin matsayi. Ayyukansa sun dawo da martabar da aka rasa a rundunar sojin kasar nan.”
A. M Yerima.
Hoton sakon da hedkwatar tsaro ta fitar da na sojan ruwa, A. M Yerima
Source: Twitter

Badaru ya yi magana kan A.M Yerima

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta kare duk wani soja da ke gudanar da aikinsa bisa doka.

Kara karanta wannan

Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri

Jawabin ministan ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa an samu cece-kuce tsakanin Ministan FCT, Nyesom Wike, da wani jami’in sojan ruwa, Lt. A.M. Yerima.

Ma'aikatar tsaron Najeriya ta bayar da tabbatar da cewa gwamnati da rundunar soji za su ci gaba da mutunta jami'ansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262