Sheikh Gumi Ya Tsere zuwa Turkey Saboda Barazanar Trump? An Ji Gaskiyar Zance

Sheikh Gumi Ya Tsere zuwa Turkey Saboda Barazanar Trump? An Ji Gaskiyar Zance

  • Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yada zargin cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya tsere daga Najeriya
  • Sun dai yi zargin cewa ya tsere ne zuwa kasar Turkiyya saboda barazanar da Donald Trump ya yi ta kawo hari a Najeriya
  • Sai dai, fitaccen malamin addinin Musuluncin ya fito ya yi magana kan jita-jitar da aka yada a kansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi martani kan rade-radin cewa ya gudu zuwa kasar Turkiyya saboda barazanar Donald Trump.

Sheikh Gumi ya gabatar da hujjoji cewa tafiyarsa zuwa kasar Turkiyya ba ta da alaƙa da wani yunkuri na guduwa daga Najeriya saboda barazanar Donald Trump, ya yi kan ‘yan ta’adda da ake zargi da kashe Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Sheikh Gumi ya musanta tserewa Donald Trump
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da Shugaba Donald Trump Hoto: Donald J Trump, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Twitter

Jaridar The Guardian ta ce wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa Sheikh Gumi ya tsere daga Najeriya bayan hotunansa sun bayyana yana cikin kasar Turkiyya.

An yada jita-jita kan Sheikh Gumi

Masu yada zargin na cewa ya tsere ne bayan Trump ya yi barazanar kai wa ‘yan ta’adda farmaki.

Wasu sun ce tunda Gumi ya taɓa yin hoto tare da ‘yan bindiga a dazuzzuka, hakan na iya zama dalilin da ya sa ya fice daga kasar nan saboda tsoron kada sojojin Amurka su kai masa farmaki.

Sai dai Sheikh Gumi, wanda har yanzu yana Turkiyya ya bayyana cewa ya dade da shirya tafiyarsa tun kafin maganganun Trump.

Wane martani Sheikh Gumi ya yi?

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya bayyana cewa:

“Na samu bizar zuwa Turkiyya a a ranar 16 ga Oktoba 2025, yayin da Trump ya wallafa sakon rashin hankali kan ‘kisan gillar Kiristoci’ a Najeriya a ranar 1 ga Nuwamba 2025."

Kara karanta wannan

Gumi ya sauya shawara game da mataki kan lauya, ya kare haduwarsa da ƴan bindiga

"Amma saboda bakin ciki, wasu suka kirkiro karya suka gaskata ta. Trump ba shi da iko a kanmu, gurbatattun zukatanku ne kawai suke tsoronsa."

A wani rubutu na daban, malamin ya ce:

“Bayan komai ya lafa, za a gane cewa zargin ‘kisan gillar Kiristoci’ a Najeriya wata dabara ce da aka tsara domin sukar dokar Shari’a da yada kyamar Musulunci.”
Sheikh Gumi ya musanta jita-jitar da aka yada a kansa
Sanannen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Sheikh Gumi ya kara da cewa maganganun Trump sun fallasa wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa da ke da ƙiyayya da addinin Musulunci da kuma kasar gaba ɗaya.

“Ba za a kara yaudararmu ba."

Har ila yau, Gumi ya bayyana cewa wani likita ya rubuto masa cewa wasu kungiyoyin Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya, na kirkirar labaran bogi kan kisan gilla ta hanyar binne akwatunan gawa marasa komai don su jawo hankalin duniya.

Gumi ya ce Musulmi zai shugabanci Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya hasashen kan shugabancin Amurka.

Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa wata rana Musulmi zai zama Shugaban Amurka, inda zai kai Musulunci har cikin Fadar White House.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

Hasashen Sheikh Gumi na zuwa ne bayan nasarar Zohran Mamdani, wanda ya zama Musulmin farko da ya lashe zaben magajin garin birnin New York, daya daga cikin manyan biranen Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng