Laftanal Yerima: Abin da Muka Sani Game da Sojan Ruwa da Ya Fatattaki Wike a Abuja

Laftanal Yerima: Abin da Muka Sani Game da Sojan Ruwa da Ya Fatattaki Wike a Abuja

  • Sojan ruwan Najeriya, Laftanar A.M. Yarima, ya zama sananne bayan fafatawar sa da Nyesom Wike a birnin tarayya Abuja
  • Yarima, ɗan asalin Kaduna, wanda ya yi karatu a ABU da NDA, ya samu yabo saboda jarumta, biyayya ga umarnin manyansa
  • Legit Hausa ta zakulo muhimman abubuwan sani game da sojan ruwa da ya hana Wike shiga wani fili a yankin Gaduwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Laftanar Ahmad M. Yarima, ya zama abin yabo da cece-kuce a Najeriya bayan rikicinsa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a Abuja ranar 11 ga Nuwamba, 2025.

An samu hayaniya a yankin Gaduwa, inda Wike da tawagarsa suka je dakatar da aikin gini a wani fili, amma sojan ruwan ya tsaya kai da fata yana kare umarnin da aka ba shi.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: An ji abin da soja ya tattauna da CDS a waya yayin rigima da Wike

An samu bayanai game da sojan ruwa da ya yi rigima da Wike a Abuja.
Hoton Laftanal Ahmad M. Yarima, sojan da ya yi takaddama da Wike a Abuja. Hoto: M. Yarima/X
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta zakulo wasu muhimman abubuwa game da wannan sojan ruwa, Laftanal Ahmad M. Yarima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin A.M Yarima daga Kaduna

Laftanal Yarima ɗan asalin Kaduna ne, wanda aka san yankinsa da fitar da shugabanni masu jajircewa da ladabi.

Ya fara karatu a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria a 2011, daga nan ya koma makarantar soji ta NDA, inda ya samu horo mai tsanani kafin a ɗora masa alamar Laftanar a rundunar sojan ruwa.

An bayyana shi a matsayin mutum mai nutsuwa, hankali da cikakken kishin aiki. Abokansa da tsofaffin abokan karatunsa sun bayyana shi da cewa “jami’i ne mai ƙwarewa da mutunci,” wanda ya kware wajen fuskantar matsin lamba ba tare da ya tsorata ba.

Aikin sa a rundunar ruwa

A matsayinsa na Laftanar (mukamin da ya yi dai dai da na Kyaftin a sojan kasa), Yarima yana da alhakin jagorancin aiki a matsakaicin matsayi na sojan ruwa.

Kara karanta wannan

Hana Wike shiga fili a Abuja, Lauya ya fadi zunubin da sojan ruwa ya aikata

Ya taba aiki a kan jirgin NNS Kada – jirgin sintiri na zamani da ake amfani da shi wajen yaki da fashi a teku da kare muhimman kayayyakin man fetur na Najeriya a yankin Gulf of Guinea.

An yaba masa da kwarewar da ya samu daga NDA da horon da ke ba shi kwarin gwiwa wajen kula da tsaro da aiki cikin natsuwa, kamar yadda aka gani a arangamarsa da Wike.

Rikicin Gaduwa: “Ni ba wawa bane, ranka ya daɗe”

Rikicin ya faru ne a wani fili mai lamba 1946 da ke Gaduwa, Abuja, wanda ake zargin tsohon hafsan sojan ruwa, Admiral Awwal Gambo, ne ya mallaka.

Rahoto ya nuna cewa Laftanal Yarima ya yi karatu a ABU Zaria sannan ya wuce makarantar sojoji ta NDA.
Hoton Laftanal Ahmad M. Yarima, sojan ruwa da ya yi rigima da Wike a Abuja. Hoto: @bossmuhadan
Source: Twitter

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Nyesome Wike ya je da jami’an FCTA da jami'an tsaro filin domin hana ci gaba da aikin gini saboda rashin izinin hukumomi.

Laftanar Yarima, wanda yake jagorantar tawagar sojojin ruwa da ke tsare wurin, ya tsaya cak ya ce yana bin umarnin manyansa, don haka ba zai bar Wike ya shiga filin ba.

Wike ya yi masa ihu tare da kiransa da “wawa,” amma Laftanal Yarima cikin ladabi ya ce, “Ni ba wawa bane, ranka ya daɗe. Ina bin umarni ne kawai.”

Kara karanta wannan

Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri

Rikicin ya kai ga Wike ya kira hafsan tsaron ƙasa da hafsan sojan ruwa, amma kafin a warware batun, bidiyon lamarin ya riga ya bazu a kafafen sada zumunta, inda al’umma da dama suka yaba da jarumtar Yarima.

'Laftanal Yarima ya take doka' - Babban lauya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Farfesa Sebastine Hon (SAN), ya ce sojan ruwa, A.M. Yerima, ya karya doka da ya yi cacar baki da ministan Abuja Nyesom Wike.

Babban lauyan ya ce babu wata doka da ta ba soja damar hana ministan Abuja shiga wani fili 'da sunan bin umarnin wani babba, don yin hakan raina ikon shugaban kasa ne.'

Farfesa Hon ya ce kotun koli ta jima da yin hukunci kan ire-iren wadannan matsaloli, kuma Laftanal A.M Yerima na iya fuskantar hukunci a kotun sojoji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com