Hana Wike Shiga Fili a Abuja, Lauya Ya Fadi Zunubin da Sojan Ruwa Ya Aikata

Hana Wike Shiga Fili a Abuja, Lauya Ya Fadi Zunubin da Sojan Ruwa Ya Aikata

  • Farfesa Sebastine Hon (SAN), ya ce sojan ruwa, A.M. Yerima, ya karya doka da ya yi cacar baki da ministan Abuja Nyesom Wike
  • Babban lauyan ya ce babu wata doka da ta ba soja damar hana ministan Abuja shiga wani fili 'da sunan bin umarnin wani babba'
  • Farfesa Hon ya ce kotun koli ta jima da yin hukunci kan ire-iren wadannan matsaloli, kuma A.M Yerima na iya fuskantar hukunci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babban Lauya kuma kwararren masani kan kundin tsarin mulki, Farfesa Sebastine Hon (SAN), yi magana kan takaddamar Nyesom Wike da wani sojan ruwa.

Farfesa Sebastine ya bayyana cewa jami’in rundunar sojan ruwa, A.M. Yerima, ya karya doka lokacin da ya cacar baki da ministan babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun taso sojan da ya kalubalanci Wike a gaba, suna neman a kori matashin a aiki

Lauya ya ce sojan ruwa da ya hana Wike shiga wani fili a Abuja ya karya doka.
Hoton ministan Abuja, Nyesom Wike da na sojan ruwa, A.M Yerima. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Twitter

Lauya ya caccaki soja kan tare hanyar Wike

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, Farfesa Hon ya ce babu wata hujjar doka da ta ba jami’in sojan ruwan damar hana Wike shiga filin da ake takaddama a kai a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A karkashin doka, soja ba zai iya hana minista shiga fili ba da sunan wai yana bin umarnin wani babban jami’in soja."

- Farfesa Sebastine Hon.

Hon ya jaddada cewa, tun da dadewa, kotun koli ta yanke hukunci cewa, bai wajaba a kan soja ya bi umarni idan wannan umarni ya sabawa doka.

Ya ambaci shari’o’i biyu; tsakanin Onunze da Najeriya (2023) da shari'ar rundunar sojojin sama da James (2002) a matsayin misalai da suka tabbatar da wannan ka’ida.

'An raina ikon shugaban kasa' - Lauya

Ya ce idan har akwai batun tsaro, tsohon jami’in soja da ke cikin takaddamar ya kamata ya kira ‘yan sanda, ba ya tura jami’an soja don kare wurin gini ba.

Kara karanta wannan

Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri

Farfesan ya kara da cewa bisa sashi na 297(2) da 302 na kundin tsarin mulkin 1999, Ministan Abuja yana da ikon shugaban kasa kan harkar filaye a Abuja.

Saboda haka, babban lauyan ya ce hana Wike shiga filin na nufin wulakanta ikon shugaban kasa da kuma tsarin farar hula, in ji rahoton Punch.

“Ko da mai ba da umarni yana kan aiki, bai da hurumin hana Wike shiga filin. Wannan raini ne ga ikon shugaban kasa."

- Farfesa Sebastine Hon.

Lauya ya ce A.M Yerima, sojan da ya tarewa Wike hanya na iya fuskantar hukunci.
Hoton ministan Abuja, Nyesom Wike da na sojan ruwa, A.M Yerima. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Jami’in sojan ruwa na iya fuskantar hukunci

Farfesa Hon ya ce Sashi na 114 na Dokar Sojoji ya bayyana cewa, za a iya gurfanar da duk jami’in soja da ya aikata laifi na farar hula a gaban kotun sojoji.

Babban lauyan ya ce jami’in sojin ruwan ya karya doka ta hanyar hana jami’in gwamnati yin aikinsa, kuma hakan zai iya laifin da kotu za ta hukunta shi a kansa.

Farfesan ya kuma gargadi jama’a da kada su yaba wa irin wannan hali, yana cewa yana iya karfafa gwiwar jami’an tsaro su raina ikon farar hula a gaba.

Kara karanta wannan

Wike ya yi magana a fusace bayan sojoji sun fatattake shi a Abuja

'Abin da ya kamata a yi wa Wike - Hikima

A wani labarin, mun ruwaito cewa, lauya a Arewacin Najeriya, Abba Hikima ya yi magana bayan rigimar da ta faru da Nyesom Wike da sojoji a Abuja.

Abba Hikima ya ce wannan matashin soja, A.M Yerima, ya cancanci a girmama shi, kuma a ba shi lambar yabo kan abin da ya yi.

Fitaccen lauyan ya kuma bayyana cewa babu wani laifi da sojan ya aikata, idan aka yi duba da cewa yana bin umarnin na sama da shi ne a aikin soja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com