'Yan APC Sun Taso Sojan da Ya Kalubalanci Wike a Gaba, Suna Neman a Kori Matashin a Aiki
- Jigon jam’iyyar APC, Joe Igbokwe, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike bayan wani jami’in soja ya yi takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Igbokwe ya zargi wasu gungun mutane masu kwace filaye da mamaye babban birnin tarayya Abuja, da cin moriyar barnar tsarin gine-gine
- Ya kuma tambayi asalin filin da ake cece-kuce a kai, yana bukatar a bayyana wanda ya mallake shi da yadda aka same shi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jigon jam’iyyar APC, Joe Igbokwe, ya yi kira da a gudanar da cikakken a kan jami’in soja, Laftanal A.M Yerima da ya yi ce-ce-ku-ce da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
A ranar Talata ne wani faifan bidiyo ya bayyana zazzafar musayar yawu a tsakanin jami'in sojan ruwan da Nyesom Wike a kan wani filin tsohon shugaban rundunar sojan ruwa, Admiral Awwal Gambo.

Kara karanta wannan
Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri

Source: Facebook
A cikin jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Igbokwe ya bayyana cewa abin da jami’in soja ya aikata rashin kunya ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya tsoma baki kan rikicin Wike
Daya daga cikin manyan 'yan jam'iyyar APC, Joe Igbokwe ya zargi Laftanal AM. Yerima da rashin girmama hukuma ba,tare da kira da a raba shi da aikinsa.
Igbokwe ya ce:
“Wannan shi ne matashin jami'in sojin ruwa, Lt. Yarima, wanda ya kalubalanci Ministan Abuja, Mai Girma Nyesom Wike. Wannan matashin jami’i bai nuna girmamawa ga hukuma ba. A kore shi daga aiki."
Jagora a APC ya dauki zafi
Igbokwe ya kuma yi zargin cewa matsalar mamayar filaye ta zama babbar barazana a Abuja, inda ya bayyana cewa wasu ƙungiyoyi masu kudi na saye filaye yadda suka ga dama.
"Na samu bayanai daga sahihan majiyoyi da suka tabbatar da cewa wasu masu kwacen filaye sun mamaye Abuja na tsawon shekaru." Harkar ta zama kasuwanci mai maiko, sun mayar da abin ko a mutu ko a yi rai."

Kara karanta wannan
'PDP ta mutu,' Fayose ya fadi sunan gwamnan PDP da zai koma jam'iyyar APC a Arewa

Source: Twitter
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa mai filin bai fito ya yi gaba da gaba da Wike da kansa ba, yana mai cewa dole ne a binciki ko filin an mallake shi bisa doka.
Jagora a APC ya nanata cewa irin wadannan abubuwa na dakile kokarin gwamnati na ganin an bi doka da oda yadda ya kamata.
Tsohon Minista ya gano kuskuren Wike
A baya, mun ruwaito cewa Tsohon ministan sufuri, Osita Chidoka, ya yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya nemi afuwa ga jami’in soja da ya zaga a Abuja.
An samu takaddama a tsakanin jami'in sojan ruwa, A.M Yerima rikicin a wani fili da ke unguwar Gaduwa, wanda ake alakanta shi da tsohon hafsan rundunar sojan ruwa, Admiral Awwal Gambo.
Chidoka ya bayyana jaddada muhimmancin bin doka da ka’ida a duk lokacin da gwamnati ko jami’an tsaro suka shiga aiki a fannin gwamnati, inda ya nemi a yi sulhu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng