'Yan Kasuwa Za Su Daina Shigo da Fetur daga Waje, Dangote Ya Sauke Farashin Mai

'Yan Kasuwa Za Su Daina Shigo da Fetur daga Waje, Dangote Ya Sauke Farashin Mai

  • Matatar Dangote ta rage farashin man fetur da ₦49 a kan kowace lita, abin da ya girgiza kasuwar sayar da mai a Najeriya
  • 'Yan kasuwar mai sun ce wannan mataki zai iya kawo ƙarshen shigo da fetur daga waje, saboda farashin Dangote ya fi rahusa
  • Amma wasu masana sun gargadi gwamnati cewa dakatar da shigo da mai gaba ɗaya zai iya haifar da karancin mai a kasuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - 'Yan kasuwar man fetur a Najeriya sun bayyana cewa suna dab da dakatar da shigo da man fetur daga kasashen waje.

A cewar 'yan kasuwar, hakan za ta faru ne bayan da matatar Dangote ta rage farashin man da take sayarwa da ₦49 a kan kowace lita.

Dangote ya sauke farashin litar fetur, wanda ya sanya farashin shi ya fi arha akan na kasar waje.
Hoton Alhaji Aliko Dangote da na wani ma'aikaci yana sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya rage farashin litar fetur

Kara karanta wannan

An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa matatar ta rage farashin man fetur din ne daga ₦877 zuwa ₦828 a kan kowace lita, wanda ke nufin raguwar kashi 5.6.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan shine karo na biyu cikin watanni uku da matatar Dangote ta rage farashin fetur domin daidaita kasuwa da inganta samar da mai a cikin gida.

A ranar Juma'a, wani dan kasuwa ya ce:

"Dangote ya rage farashin da yake sayar wa 'yan kasuwa mai daga ₦877 zuwa ₦828 a kan kowace lita."

Kungiyar manyan 'yan kasuwar makamashi ta Najeriya ta tabbatar da wannan ragin farashin litar fetur da matatar Dangote ta yi.

Raguwar farashin ta girgiza masu shigo da mai

Ranar Litinin, manyan 'yan kasuwa da dillalan mai sun tabbatar da cewa sabon farashin Dangote ya canza tsarin kasuwa gaba ɗaya, domin yanzu man da ake shigo da shi daga waje ya fi tsada.

Sakataren kungiyar MEMAN, Clement Isong, ya ce wannan canjin zai sa ba zai yiwu a ci gaba da shigo da mai daga waje ba.

“Za a daina shigo da mai yanzu saboda farashin shigo da shi ya fi na Dangote tsada. Wannan ita ce gaskiyar lamarin,” in ji Isong.

Kara karanta wannan

'Fetur zai rage kudi': IPMAN ta fadi yadda Dangote zai sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya

Ya bayyana cewa matatar Dangote tana da ‘yancin saita farashin sa bisa tsarin kasuwa, musamman la'akari da farashin da ake kashewa wajen shigo da mai daga waje zuwa Najeriya.

Msana na ganin cewa dains shigo da fetur daga kasashen waje zai iya jawo karancin mai a Najeriya.
Dandazon mutane na kokarin sayen fetur daga wani gidan mai. Hoto: Getty Images.
Source: UGC

Kada a daina shigo da mai gaba ɗaya

Sai dai wasu ‘yan kasuwa sun ja hankalin gwamnati cewa shigo da mai daga kasashen waje har yanzu yana da mahimmanci domin kauce wa karancin mai a wasu lokuta.

Sun ce dakatar da shigo da man gaba ɗaya na iya jawo cunkoso a tashoshin mai da hauhawar farashi idan samar da cikin gida bai wadatar ba.

Jaridar Punch ta rahoto wani mai kasuwanci da fetur ya ce:

“Dangote na iya rage farashi, amma ba lallai ya iya samar da man da zai ishi kasar gaba ɗaya ba. Idan aka daina shigo da mai, akwai yiwuwar karancin mai a wasu jihohi.”

Gwamnati ta kara harajin shigo da man fetur

Tun da fari, mun ruaito cewa, gwamnatin tarayya ta sanya harajin kashi 15 cikin 100 kan shigo da man fetur da dizal da aka tace daga kasashen waje.

Ana tunanin sabon tsarin zai iya haifar da karin farashin litar man fetur da N150, duk da cewa gwamnati ta ce tasirin ba zai wuce N100 ba.

Kara karanta wannan

ISWAP: Masu hidimar kasa, NYSC sun tsallake rijiya da baya a Borno

Shugaban kasa ya umurci hukumomin da abin ya shafa su fara aiwatar da tsarin nan take, maimakon jiran wa’adin kwanaki 30 da aka tsara tun farko.

"Litar fetur za ta koma N700" Alhaji Kabir.

A zantawar Legit Hausa da wani manajan gidan man Shade da ke Kaduna, Alhaji Mubarak Aliyu, ya shaida mana cewa ana samun saukin fetur a yanzu, ta dalilin matatar Dangote.

Alhaji Mubarak ya ce:

"Idan har matatar man Dangote za ta ci gaba da sauke farashin mai idan an samu saukar shi a duniya, to tabbas litar fetur za ta koma ƙasa da N700.
"Ana ci gaba da samun kasashen da ke hako mai, kasuwar duniya na ganin karuwar danyen mai, sannan kasashe da dama sun koma tace man su, dole farashi ya sauka.
"Sannan kamar yadda IPMAN ta fada, idan har ƴan kasuwa za su samu mai kai tsaye daga matatar, to ka ga an huta da biyan kudin jigila, an huta da biyan kudin masu defo, yanzu a gidajen mai kawai za a rika sauke wa, nan ma farashin zai sauka sosai."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki motoci 5, sun sace bayin Allah a Kogi

'Litar fetur za ta haura N1,000' - 'Yan kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dillalan mai sun zargin gwamnatin tarayya da sanya sabon harajin 15% kan shigo da fetur don hana shigo da shi baki daya.

Sakataren kungiyar MEMAN, Clement Isong, ya bayyana cewa wannan dabara da gwamanti ta bullo da shi zai jawo tashin farashin litar mai.

Clement Isong ya ce suna ganin idan har lamarin ya cigaba a haka, farashin litar man fetur zai kai kusan N1,000 yayin da farashin dizal zai haura N1,100.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com