Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Halin da ake Ciki kan Tattaunawa da Amurka
- Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka na haifar da sakamako mai kyau tun bayan kalaman Donald Trump
- An shiga zaman dar-dar a kasar nan bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa zai iya kawo hari ta sama ko kasa zuwa Najeriya
- Ya bayyana haka ne bisa zargin cewa an ware kiristoci, sannan ana masu kisan kare dangi saboda kin addininsu kawai, lamarin da Najeriya ta karyata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tattaunawar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka na haifar 'da mai ido.
An fara tattaunawa domin inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bayan Amurka ta sako Najeriya a gaba, inda ta fake da batun yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Kara karanta wannan
Barazanar Trump: Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka, an ji halin da ake ciki

Source: UGC
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a Mohammed Idris, ya ce an buɗe hanyoyin sadarwa kuma ana tattaunawa cikin fahimtar juna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka
Arise News ta ruwaito cewa Amurka ta fara barazanar daukar matakin da ta yi ikirari ne saboda samun bayanai ba daidai ba a kan rashin tsaro a kasar nan.
A kalamansa:
“Yawancin rashin fahimtar da aka samu a baya ya samo asali ne daga rashin cikakken sani kan bambance-bambancen da kalubalen da muke fuskanta a gida (Najeriya).”
Ministan ya kuma bayyana cewa bincike ya nuna akwai alaƙa tsakanin wata ƙungiyar ‘yan tawaye da aka haramta a Najeriya da wasu ƙungiyoyin kamun kafa da ke Amurka.
Kuma suna kokarin fito da bayanan bogi a kan halin da Najeriya ke ciki, wanda haka ne ya jawo Amurka ta fusata har ta sanya Najeriya a cikin jerin kasashen da ake tauye hakkin kiristoci.

Kara karanta wannan
Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Sanatan Amurka ta yi korafi a kan Najeriya
Sai dai Sanata Bill Huizenga daga Amurka ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda gwamnati ke kallon hare-haren da ake kai wa Kiristoci.

Source: Twitter
Huizenga ya ce ya yi magana da shugabannin addini da mazauna ƙauyuka da aka kai hari, waɗanda suka bayyana yadda ake kashe su.
Sanata Huizenga ya ƙara da cewa rashin tsaro na ci gaba da barazana ga ci gaban tattalin arziki da saka hannun jari na waje a Najeriya.
Ya ce:
“Idan ba za ka iya tabbatar da tsaron ma’aikata ko kasuwanci ba, akwai matsala."
An shawarci jama'a kan barazanar Trump
A baya, mun wallafa cewa Ministan yada labarau, Mohammed Idris, ya roƙi ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu yayin da ake samun takaddamar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka.
Ministan ya jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu na da cikakken ƙwazo da ƙwarewa wajen kare muradun ƙasa da gyara dangantaka da sauran ƙasashe duk da barazanar da ake yi wa kasar.
Sabuwar takaddamar ta samo asali ne daga kalaman da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya wallafa kan cewa Kiristoci a Najeriya suna fuskantar kisan kare dangi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
