‘Abin da Ya Kamata a Yi Wa Wike’: Lauya a Kano bayan Minista Ya Kacame da Soja
- Lauya Abba Hikima ya goyi bayan matashin sojan da ya samu sabani da Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Hikima ya ce sojan ya bi umarnin shugaban ƙasa ne, don haka abin da Wike ya yi masa saba wa doka ne
- Lauyan ya ƙara da cewa maimakon a hukunta sojan, kamata ya yi a girmama shi da ba shi lambar yabo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Fitaccen lauya a Arewacin Najeriya, Abba Hikima ya yi magana bayan rigimar da ta faru da Nyesom Wike da sojoji a Abuja.
Hikima ya tsage gaskiya game da iyakar sojoji da kuma shi kansa Nyesom Wike inda ya kawo bayanai kan tsarin doka game da lamarin.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da ya yi hira da DCL Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook a yau Laraba 12 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Hikima ya yabawa matashin soja
A yayin hirar, Hikima ya ce wannan matashin soja kamata ya yi a girmama shi da kuma ba shi lambar yabo kan abin da ya yi.
Ya ce:
"Wannan matashin soja kamata ya yi a girmama shi, a ba shi lambar yabo, idan akwai wani abu na laifi bai wuce gadi da aka saka shi ba domin gadi ba aikin soja ba ne.
"Sai idan ba laifi ba ne hakan, kuma an ce masa je ka yi to ba matsala ba ne, laifi shi ne misali a ce je ka kashe mutane ba su yi komai ba.
"Abu ne marar dadi, Wike shi ne minsitan Abuja kuma babban mutum ne, kamar yadda gwamnoni ke da jihohi haka shi me ke da Abuja."

Source: Facebook
Wane laifi matashin sojan ya aikata?
Abba Hikima ya ce babu wani laifi da sojan ya yi duba da cewa shi yana bin umarni da na shugaban kasa wanda shi ne kololuwa.
Lauyan ya ce abin da Nyesom Wike ya yi kai tsaye saba doka ne kuma ya cancanci a hukunta shi saboda cin zarafin sojan da ya yi.
"Haka kuma sojoji wakilai ne kai tsaye na shugaban kasa, a ka'idar aikin soja duk lokacin da na gaba da kai ya ba ka umarni idan bai saba doka doka ba, yana ba ka umarni ne na shugaban kasa.
"Abin da Wike ya yi kai tsaye saba doka ne, ka kalli mutum yana aiki na kasa ka kira shi da wannan suna saba doka ne, kuma abin da Wike ya yi za a iya hukunta shi."
- Abba Hikima
Tsohon minista ya soki Wike kan rigima da soja
Kun ji cewa tsohon ministan sufuri a Najeriya ya tsoma baki kan ta kaddamar da ta faru tsakanin Nyesom Wike da sojoji a Abuja.
Osita Chidoka ya ce cin zarafin jami’in tsaro na nufin raina ikon kasa, yana mai gargadin cewa gwamnati ta dogara da doka ba faɗa a titi ba.
Ya ce Wike ya yi kuskure da shiga lamarin kai tsaye, yana kira ga jami’an tsaro su daina ƙara rikici a irin waɗannan yanayi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
