Amaechi Ya Faɗi Yadda na Kusa da Buhari Suka Hana Ruwa Gudu domin Inganta Zabe
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana damuwa kan maganar gyaran tsarin zabe da kullum ake yi
- Amaechi ya ce wasu cikin gwamnatin Buhari sun hana aiwatar da gyaran zabe da tsohon shugaban kasar ya shirya
- Ya bayyana cewa waɗanda suka hana wannan gyara suna cikin gwamnati yanzu, yana mai cewa al’umma ce kawai za ta iya kawo sauyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana hanyar da za a kawo sauyi cikin sauki a zabubbuka a Najeriya.
Amaechi ya ce akwai wasu a cikin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da suka hana gyaran zabe.

Source: Facebook
Amaechi ya fadi abin da zai kawo sauyi
Amaechi ya bayyana hakan ne a taron gyaran zabe da aka gudanar a Abuja a jiya Talata 11 ga watan Nuwambar 2025, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan a gwamnatin Buhari ya ce gyaran zabe mai ma’ana zai gudana ne idan ‘yan ƙasa suka jagoranta.
Ya ce:
“Yawancin ‘yan Najeriya suna goyon bayan gyaran zabe ne idan abin zai amfani cikinsu. Idan suna cin gajiyar gwamnati, sai su yi shiru.”
Amaechi ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda suka hana Buhari yin gyaran suna cikin gwamnati yanzu, yana mai sukar irin wannan halin.
Ya ce dole ne ‘yan ƙasa su fito kwansu da kwarkwata domin hana magudin zabe, saboda babu wanda zai iya sace sakamako idan jama’a suka fito.

Source: Twitter
Shawarar Amaechi ga yan kasa kan sauyi
Tsohon ministan ya nuna takaici cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da Emeka Anyaoku ba su halarci taron ba duk da an gayyace su.
Amaechi ya ce sakamakon taron ba zai haifar da wani tasiri ba idan al’umma ba su bukaci gyaran zabe kai tsaye daga ƙasa ba.
A cewarsa:
“Abin da zai haifar da sauyi shi ne idan mu duka ‘yan ƙasa muka ce ya isa, dole a kawo sauyi yanzu.”
Ya kuma yi suka ga yadda kungiyoyin ma’aikata da dalibai ke shiga siyasa ta hanyar goyon bayan gwamnati mai ci don kare matsayinsu, cewar TheCable.
A nata bangare, Oby Ezekwesili ta ce tun daga 1999 Najeriya ta kasa bin ma’aunin dimokuradiyya saboda rashin shari’ar gaskiya ga masu laifin zabe.
Ta ce:
“Rashin bincike da hukunci kan laifukan zabe ya sa ba a tsoron aikata laifuffuka da kawo cikas a tsarin zabe na Najeriya.”
Ezekwesili ta roki gwamnati ta bai wa hukumar INEC ikon gurfanar da masu laifin zabe kai tsaye domin tabbatar da gaskiya da ladabtarwa.
Amaechi ya magantu kan kifar da Tinubu
A wani labarin, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bukaci jam’iyyun adawa su tashi tsaye su shirya kafin babban zaben 2027.
Ya ce za a iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben mai zuwa, amma dole sai idan ‘yan ƙasa sun fito kwansu da kwarkwata.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
Amaechi ya ce NLC, ASUU ko NANS kadai ba za su iya ba, dole sai jama'a sun dauki nauyin kare dimokuradiyya da kansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

