Yadda aka Yi wa Wike Rubdugu kan Gardama da Sojojin Najeriya a Abuja

Yadda aka Yi wa Wike Rubdugu kan Gardama da Sojojin Najeriya a Abuja

  • Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da lauyoyi sun yi wa Nyesom Wike rubdugu kan gardamar da ya yi da wani soja a Abuja
  • Sun ce halin da ya nuna ya saba da mutuncin ofishin gwamnati kuma ya nuna rashin girmama rundunar soja
  • Sun bukaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ja kunnen ministan don kauce wa sake faruwar irin wannan lamari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu lauyoyi da ƙungiyar kare haƙƙin jama’a sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi faɗa da jami’in soja kan wani fili.

Lamarin dai ya faru ne a kan wani fili a Gaduwa da ke Abuja, wanda ake cewa na tsohon hafsan rundunar sojin ruwa ne, Awwal Zubairu Gambo (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri

Nyesom Wike
Nyesom Wike yayin rigima da sojoji a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar CISLAC ƙarƙashin jagorancin Auwal Musa Rafsanjani ta soki yadda ministan ya gudanar da lamarin, tana cewa abin da ya aikata abin kunya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an FCTA sun je rusa wani gini ne sai wasu sojoji suka hana su, abin da ya jawo gardama tsakanin ministan da jami’in soja a bainar jama’a inji rahoton Punch.

CISLAC ta zargi Wike da cin zarafin soja

Rafsanjani ya bayyana cewa yadda Wike ya yi wa jami’in soja ihu a bainar jama’a ya zama “cin zarafin rundunar soja” da kuma “rashin girmama tsarin gwamnati.”

Ya ce:

“Wike ya zubar da mutuncin ofishin gwamnati. Ba zai yiwu a ci gaba da gudanar da aiki da irin wannan dabara ta tashin hankali ba.”

Ya ƙara da cewa, ya kamata ministan ya nemi hanyar diflomasiyya da bin ƙa’ida wajen gudanar da ayyukan sa.

“Shugaban ƙasa bai ba Wike mukami don ya rika kwace filaye da faɗa da jami’an gwamnati ba. Muna kira ga shugaban ƙasa ya ja kunnen Wike saboda halinsa yana bata sunan gwamnati,”

Kara karanta wannan

Wike ya yi magana a fusace bayan sojoji sun fatattake shi a Abuja

Inji shi

Rafsanjani ya kuma nuna damuwa cewa irin wannan hali na iya rage kwarin gwiwar jama’a ga hukumomin gwamnati, yana mai cewa:

“Mun ga ministoci da dama a baya, amma babu wanda ya nuna irin wannan hali.”

Lauyoyi sun soki Wike kan rigima da soja

Babban lauyan, Dayo Akinlaja (SAN), ya bayyana cewa wannan rikici ya nuna matsalar tsarin gudanarwa a ƙasar, yana mai cewa:

“Za a iya magance wannan lamari cikin sauƙi. Amma an bar tashin hankali ya maye gurbin bin doka.”

Haka nan, lauya Jibrin S. Jibrin ya ce halin da ministan ya nuna bai dace ba, domin akwai tanade-tanaden doka da ke bayyana yadda ake magance irin waɗannan rikice-rikice.

Wike na gabawa da 'yan jarida
Yadda Wike ya yi hira da 'yan jarida bayan gardama da sojoji a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook
“Idan an bi hanya ta doka, ba sai an kai ga irin wannan rigima a bainar jama’a ba,”

Inji lauyan

Buratai ya gargadi Wike kan fada da soja

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban sojojin kasan Najeriya, Tukur Buratai ya yi magana kan gardamar da Wike ya yi da sojoji.

Kara karanta wannan

Takaddama da soja: Tsohon minista ya gano kuskuren Wike, ya ba shi shawara

Buratai ya bukaci Nyesom Wike ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu hakuri tare da sojan da ya yi cacar baki da shi.

A cewar Buratai, gardama da dakarun sojojin Najeriya ba abu ne da za a lamunta ba, musamman daga 'yan siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng