Buratai Ya Gargadi Wike kan Rigima da Soja, Ya Nemi Ministan Abuja Ya ba da Hakuri

Buratai Ya Gargadi Wike kan Rigima da Soja, Ya Nemi Ministan Abuja Ya ba da Hakuri

  • Tsohon hafsan sojan Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya zargi ministan Abuja, Nyesom Wike, da cin zarafin jami’in soja
  • Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga tsaron ƙasa da kuma tauye martabar dakarun Najeriya
  • A bayanin da ya yi, Buratai ya nemi Nyesom Wike da ya nemi afuwa daga shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma jami’in da abin ya shafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya soki ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike bisa yadda ya yi jayayya da wani jami’in soja a Abuja.

Lamarin ya faru ne saboda wani rikici kan fili da ake ce-ce-ku-ce a kai a babban birnin ƙasar da aka ce na wani babban soja ne.

Kara karanta wannan

Wike ya yi magana a fusace bayan sojoji sun fatattake shi a Abuja

Nyesom Wike, Tukur Buratai
Hoton Wike da sojan Najeriya da Tukur Buratai. Hoto: Lere Olayinka|Lere Olayinka
Source: Facebook

Tukur Buratai ya yi martanin ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan bidiyon Wike da sojan ya karade kafafen sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata ne aka hango Nyesom Wike yana gardama da wani jami’in sojan ruwa da ke bakin aiki a Abuja.

Buratai ya bayyana cewa hakan ya zama abin takaici da ke iya lalata tsarin tsaro da girmamawar da ake baiwa jami’an soja.

Buratai ya zargi Wike da keta dokar soja

Buratai ya ce kalaman Wike sun wuce cin zarafi, domin sun nuna raini ga tsarin aikin soja da kuma umarnin shugaban ƙasa.

The Cable ta rahoto ya bayyana cewa:

“Caccakar jami’in soja a bainar jama’a ba kawai rashin ladabi ba ne, illa ce da ke lalata tsarin aikin da rundunar ke aiki a karkashinsa.”

Ya ƙara da cewa, irin wannan hali na iya rage ƙarfin gwiwar dakarun da ke sadaukar da rayukansu wajen kare martabar Najeriya da tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sabon ministan jin kai ana cikin neman a biya kudin N Power

Wike yayin gardama da soja
Sojan da Wike ya yi gardama da shi a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook
“Abin da Wike ya aikata yana iya haifar da rashin kwanciyar hankali a tsakanin jami’an tsaro, domin yana iya tauye darajar da ke tsakanin kwamandoji da ma’aikata a fagen soja,”

Inji Buratai

Buratai ya nemi Wike ya ba da hakuri

Buratai ya nemi Wike da ya fito fili ya nemi afuwa daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne kwamandan dakarun Najeriya, da kuma daga jami’in da ya ci zarafinsa a bainar jama’a.

“Dole ne Wike ya fahimci cewa wannan lamari ba batun siyasa ba ne, batun kare tsarin doka da oda ne. Ba za mu yarda wani mai mukami ya raina jami’in soja a bainar jama’a ba,”

Inji tsohon hafsan

Martanin Wike bayan rigima da soja

A wani rahoton, mun kawo muku cewa ministan FCT, Abuja ya yi magana bayan hayaniya da ya yi da wasu sojoji.

Nyesom Wike ya bayyana cewa ba zai lamunci hana shi shiga wani fili da wasu sojoji suka yi ba a Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Wike ya gamu da gamonsa, soja ya ki bari ya tozarta shi a bainar jama'a

Ministan ya ce wani babban jami'in soja ne da ya yi ritaya ya ke kokarin gini ba tare da izini ba a filin da ake rikici a kansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng