Wike Ya Yi Magana a Fusace bayan Sojoji Sun Fatattake Shi a Abuja
- Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gana da manema labarai bayan cacar baki da sojojin Najeriya kan fili
- Ya ce babu wanda zai yi amfani da matsayinsa na baya a gwamnati don tsoratar da hukumomin FCTA
- Wike ya umarci a dakatar da duk wani gini ko cigaba aikin da ake yi ba tare da izini ba a filin da ake rikici a kai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira da “mamayar sojoji” kan wani fili da ake rikici a kansa a Abuja.
Wike ya kai ziyara kai tsaye zuwa wurin a ranar Talata bayan samun rahoto cewa wasu sojoji sun kori jami’an hukumar raya birane ta FCTA da ke aikin hana gini ba bisa ka’ida ba.

Source: Facebook
A sakon da hadiminsa ya wallafa a X, Wike ya gargadi masu amfani da ƙarfin soja don hana gwamnati aiwatar da doka, yana mai cewa ba zai lamunci irin wannan rashin da’a ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kori jami’an FCTA a Abuja
Wike ya ce jami’an sashen kula da raya birane sun je wurin domin aiwatar da umarninsa na hana gini, amma wasu sojoji da ake zargin suna aiki da umarnin tsohon hafsan soja suka kore su.
“Ina ofis aka kira ni cewa sojoji sun mamaye wurin,”
Inji shi.
Ya kara da cewa:
“Lamarin abin takaici ne sosai.”
Ya ce ya yi mamaki cewa tsohon babban jami’in soja zai nuna karfi maimakon bin matakan doka da suka dace.
“Ba zan lamunci tsoratarwa ba” — Wike
Ministan ya ce bai fahimci yadda mutum da ya taba rike mukamin soja mafi girma zai kasa zuwa ofishinsa domin tattaunawa ba, sai dai ya nemi amfani da soja don tsoratar da hukumomi.
“Ni bana cikin wadanda za su lamunci barazana,”
Inji Wike cikin tsawa.
“Ba za mu bari rashin doka ya mamaye FCT ba.”
Ya kara da cewa jami’an hukumar raya birane sun bukaci masu ginin su kawo takardu ko izinin mallaka, amma ba su da ko daya.

Source: Facebook
Wike ya koka kan rashin bin doka
Wike ya ce babu wani tsarin doka da aka bi wajen mallakar filin, domin babu rajista, babu amincewar gwamnati, kuma babu izinin gini.
“Idan muka ci gaba da barin irin wannan rashin doka, yaya sauran ‘yan kasa masu biyayya ga doka za su ji?”
Inji shi
Ya kuma bayyana cewa tuni ya tuntubi hafsan tsaron kasa da hafsan rundunar sojan ruwa, wadanda suka tabbatar masa cewa za a magance matsalar cikin lumana.
Wike ya yi cacar baki da soja a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa ministan birnin tarayya, Nyesom Wike ya yi cacar baki da wani sojan Najeriya a Abuja.
Wike ya bukaci shiga wani fili da ake gini a Abuja amma sojan ya ce ba zai shiga ba, lamarin da ya jawo jayayya.
Daga karshe, bayan doguwar muhawara, Wike da tawagarsa sun tafi daga wajen ba tare da shiga filin da ake aikin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


