Barawo da Karfin Hali: Wani Mutum Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano, Ya Sace Mota
- Wani barawo ya shiga fadar gwamnatin jihar Kano da asuba a ranar Litinin, ya sace motar Toyota Hilux daga cikin jerin motocin mataimakin gwamna
- Rahotanni sun nuna cewa barawon ya shiga gidan gwamnati ta ƙofa ta huɗu ya kuma fita da motar ta babbar ƙofa bayan 5.00 na safe
- Tuni dai aka fara bincike tare da tsare direban motar na ɗan lokaci, yayin da jami’an tsaro ke nazarin bidiyon CCTV domin gano wanda ya yi satar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani barawon mota ya shiga Fadar Gwamnatin Jihar Kano da sanyin safiyar Litinin, inda ya yi awon gaba da motar Toyota Hilux.
Rahotanni sun nuna cewa barawon ya samu shiga Fadar ta Gwamnati ta Kofa ta 4, sannan ya fita da motar kusan 5.00 na safiyar Litinin.

Kara karanta wannan
Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

Source: Facebook
Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa majiyoyi daga cikin Fadar sun bayyana cewa, bayan an duba bidiyon CCTV, an gano yadda barawon ya fice da motar ta babbar kofar shiga gidan gwamnatin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi satar mota a gidan gwamnatin Kano
Majiyoyin sun ƙara da cewa motar da aka sace na cikin jerin motocin rakiyar Mataimakin Gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo.
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa ofishin Mataimakin Gwamna baya samun tsaro sai dai a lokutan aiki ko idan Mataimakin Gwamnan yana ofis.
A cewar majiyar, bayan an gano cewa an sace motar ne aka tsare direbanta mai suna Shafiu Sharp-Sharp, tare da ui masa tambayoyi, sannan aka tsare shi na ɗan lokaci.
Ana neman motar gidan gwamnatin Kano
Wata majiyar ta kara da cewa tuni bincike ya yi nisa, inda aka sanar da jami'an tsaro bayanan motar yayin da ake tsananta bincike.
Majiyar ta ce ana sa ran jami'an tsaro za su sanya idanu domin damke motar da wanda ya iya shiga cikin gidan gwamnati domin aikata wannan sata.

Kara karanta wannan
Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025

Source: Facebook
A cewar majiyar:
“An riga an fara bincike. Ana ci gaba da tambayar direban, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke nazarin bidiyon CCTV."
“An kuma bai wa jami’an tsaro cikakken bayanin motar da aka sace domin su kama ta tare da damke barawon."
Zuwa yanzu, Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa bai ce komai a kan batun sace motar ba.
Ganduje ya hadu da gwamnan Kano, Abba
A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, sun haɗu karo na farko tun bayan zaben 2023.
Ganawar ta faru ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda suka yi musayar gaisuwa cikin natsuwa da annuri a fuskokinsu, yayin da aka hango Ganduje ya fada wa Abba wata magana.
Wannan haɗuwa da ta kasance ta bazata, ta nuna alamun mutunta juna da kyakkyawar mu’amala tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar duk da zafin adawar siyasarsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
