Takaddama da Soja: Tsohon Minista Ya Gano Kuskuren Wike, Ya ba Shi Shawara
- Tsohon ministan sufuri a Najeriya ya tsoma baki kan ta kaddamar da ta faru tsakanin Nyesom Wike da sojoji a Abuja
- Osita Chidoka ya ce cin zarafin jami’in tsaro na nufin raina ikon kasa, yana mai gargadin cewa gwamnati ta dogara da doka ba faɗa a titi ba
- Ya ce Wike ya yi kuskure da shiga lamarin kai tsaye, yana kira ga jami’an tsaro su daina ƙara rikici a irin waɗannan yanayi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ministan sufuri, Osita Chidoka, ya yi magana kan abin da ya faru da Nyesom Wike da sojoji.
Tsohon ministan ya bukaci ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya nemi afuwa ga jami’in soja da ya zaga a rikicin da ya faru.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani rubutu da Chidoka ya yi a shafinsa na Facebook a jiya Talata 11 ga watan Nuwambar shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arangamar Nyesom Wike da sojoji a Abuja
Rahotanni sun ce fadan ya faru ne a wani fili da ke unguwar Gaduwa, inda aka ce filin na da alaƙa da tsohon hafsan rundunar sojan ruwa.
Wike da jami’an FCDA sun ziyarci wurin don dakatar da ginin da ya kira “ba bisa ka’ida ba”, inda ya sami jami’in soja a wurin.
A wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an nuna Wike cikin fushi yana cewa ko da hafsan sojan ruwa ne, dole a bi doka.
Jami’in sojan ya ce filin na tsohon hafsan soja ne, kuma suna da izini don kare shi ba wai sun zo domin ta da tarzoma ba ne.
Lamarin ya jawo maganganu a kafofin sadarwa inda wasu ke yabon sojan yayin wasu ko ke nuna cewa Wike yana iko kan abin da ya yi.

Source: Facebook
Shawarar da tsohon minista ya ba Wike
Sai dai Chidoka ya ce duk wani jami’in tsaro yana wakiltar ikon shugaban kasa da gwamnatin tarayya, don haka ba daidai ba ne a zage su a bainar jama’a.
Ya bayyana cewa irin wannan hali yana raunana ginshiƙan mulkin dimokuraɗiyya, domin gwamnati tana aiki ta hanyar dokoki da cibiyoyi, ba kai tsaye daga jami’an gwamnati ba.
Chidoka ya ce jami’an DSS da ke rakiyar Nyesom Wike ya kamata su kwantar da hankali a irin wannan lokaci, ba su ƙara rikici ba.
Ya bayyana lamarin a matsayin darasi ga shugabanci, yana mai cewa Wike ya rage darajar kujerarsa, kuma dole ne ya nemi afuwa ga jami’in da abin ya shafa.
Kalaman Wike bayan rigima da sojoji
Mun ba ku labarin cewa ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gana da manema labarai bayan cacar baki da sojojin Najeriya kan fili.
Wike ya ce babu wanda zai yi amfani da matsayinsa na baya a gwamnati don tsoratar da hukumomin FCTA.
Ministan ya umarci a dakatar da duk wani gini ko cigaba aikin da ake yi ba tare da izini ba a filin da ake rikici a kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
