Tinubu Ya Nada Sabon Ministan Jin Kai Ana cikin Neman a Biya Kudin N Power

Tinubu Ya Nada Sabon Ministan Jin Kai Ana cikin Neman a Biya Kudin N Power

  • An tabbatar da cewa Bernard Doro ne wanda Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ma'aikatar jin kai da yaki da talauci ta Najeriya
  • Doro ya kama aiki a sabon ofishinsa bayan ya isa harabar ma'aikatar da ke Abuja yau Talata, 11 ga watan Nuwamba, 2025
  • Sabon ministan ya yi alkawarin tallafa wa yan Najeriya da ke fama da talauci domin su fita daga kangin da suke ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bernard Doro ya kama aiki a hukumance a matsayin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci a ranar Talata, bayan nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa.

Ya zama minista na huɗu da zai shugabanci ma’aikatar tun bayan ƙirkirarta, inda ya gaji Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda yanzu shi ne shugaban APC na ƙasa.

Kara karanta wannan

Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja

Bernard Doro.
Hoton sabon ministan harkokin jin kai, Bernard Doro a ofis a Abuja Hoto: @fmha_pa
Source: Twitter

Sabon ministan jin kai ya kama aiki

The Nation ta ce Doro da matarsa, Dr. Naomi Doro, da wasu baki masu fatan alheri sun samu tarba daga karamin ministan jin kai, Dr. Yusuf Sununu, babban sakatare, Dr. Yakubu Kofarmata, tare da sauran ma’aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon ministan ya kama aiki ne a daidai lokacin da matasa yan N-Power ke ci gaba da kiraye-kirayen a biya su hakkokinsu da aka rike.

Da yake jawabi ga ma'aikata da shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashinsa, Doro ya yi alkawarin tallafa wa sama da kashi 60 na ‘yan Najeriya da ke fama da talauci.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ma’aikata domin cimma manufar Shugaba Tinubu ta “Renewed Hope.”

Doro ya sha alwashin kawo sauyi

“Na zauna Burtaniya sama da shekaru 20, don haka akwai ɗan gyaran da zan yi. Amma ina da yakinin cewa da haɗin kai, gogewarku da ilimin ku, za mu ɗaga darajar wannan ma’aikata,” in ji Doro.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

"Mutane da yawa suna da tsammani a kaina, ban san dalili ba, amma zan yi aiki tuƙuru don in kai ko rabin abin da ake tsammani daga gare ni. Ina fatan tare za mu iya cimma fiye da haka.”
“Shugaban ƙasa na son farfaɗo da fatan ‘yan Najeriya, musamman masu ƙaramin ƙarfi. Bisa ga ƙididdiga, sama da kashi 60% na ‘yan ƙasa suna cikin talauci iri-iri, dole mu taimaka musu.”

- Bernard Doro.

Bola Tinubu da Doro.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sabon ministan jin kai, Bernard Doro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Doro ya kuma bayyana cewa amana da haɗin kai sune za su zama ginshiƙan da za su taimaka wajen cimma burin ma’aikatar jin kai, rahoton Leadership.

“Na ji kamar a gida nake, na ji daɗin karɓar da aka yi min. Ina fatan zan fahimci al’adun wannan ma’aikata kuma in zama ɓangare na wannan al’ada.
"Duk abin kirki da na tarar, za a ci gaba da shi, amma inda ake buƙatar gyara, za mu sake fasalin al’amura," in ji shi.

Wani matashi daga cikin wadanda suke bin bashin kudin N-Power, Abdulhafiz Tukur ya bukaci gwamnatin tarayya ta biya su hakkokinsu.

Da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa kan nadin sabon minista, ya ce gwamnati ta yi alkawari ba daya ba kuma ba biyu ba amma har yanzu shiru kake ji.

Kara karanta wannan

'Ka nemi kashe ni,' Wike ya yi martani mai zafi ga Buratai bayan rigima da soja

"Muna masa fatan alheri kuma muna fatan ya duba tsofaffin 'yan N-Power ya biya su hakkokinsu, ministan da ya sauka ya mana alkawari a kasafin kudin 2025 amma har yau shiru.
"Muna kira ga gwamnati ta biya mu kudin watannin da aka rike mana, hakan zai taimaka wa matasa iri na da dama," in ji shi.

Tinubu ya tura tawaga zuwa Landan

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da Birtaniya domin dawo da Sanata Ike Ekweremadu gida Najeriya ya karisa hukuncin zaman gidan yari.

Shugaba Tinubu ya tura wata tawagar mai karfi da ta kunshi ministoci domin duba yiwuwar dawo da sanatan gidan yarin Nageriya.

Kotun Landan ta yanke masa hukuncin shekaru tara da watanni takwas a gidan yari a watan Maris 2023, bayan kama shi da laifin kokarin cire sassan jikin dan adam.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262