Barazanar Trump: Gwamnatin Najeriya Ta Fara Tattaunawa da Amurka, An Ji Halin da Ake Ciki

Barazanar Trump: Gwamnatin Najeriya Ta Fara Tattaunawa da Amurka, An Ji Halin da Ake Ciki

  • Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawar diflomasiyya da Amurka domin warware rudanin kashe-kashen da ake a Najeriya
  • Hakan dai ya biyo bayan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi cewa sojojin Amurka na iya kawo farmaki don kare kiristoci
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bukaci Amurka ta hada kai da Najeriya wajen yaki da ta'addanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta fara tattaunawa da kasar Amurka kan zarge-zargen kisan kiristoci.

Hakan dai ya biyo bayan matakin da shugaban Amurka, Donald Trump ya dauka na sanya Najeriya a jerin kasashen da ake tauye yancin addini.

Mohammed Idris.
Hoton Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris Hoto: Mohammed Idris
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta rahoto cewa gwamnatin Najeriya ta fara zaman tattaunawa da gwamnatin Amurka domin fayyace gaskiya da warware sabanin fahimtar da aka samu.

Kara karanta wannan

"Ina matashi dan Shekara 40," Obasanjo ya tuna zaman da ya yi da Amurka a mulkin soja

Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka

Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ya ce an fara tattaunawar diflomasiyya domin warware rudanin da ya shiga tsakanin Najeriya da Amurka kan batutuwan tsaro da hakkokin ɗan adam.

Mohammed Idris ya bayyana hakan a hirar da aka yi da shi a shirin The World With Yalda Hakim na tashar Sky News da aka watsa a daren Litinin.

Ya tabbatar da cewa an bude kofar sadarwa a hukumance tsakanin Abuja da Washington, yana mai cewa tattaunawa na gudana cikin kwanciyar hankali.

Shin Amurka ta fara fahimtar Najeriya?

Haka kuma ya ce wannan tattaunawa na taimakawa wajen fayyace wasu kurakurai da rashin fahimta game da halin tsaron da Najeriya ke ciki.

“An bude hanyoyin sadarwa tsakaninmu da su, kuma zan iya tabbatar da cewa mun fara tattaunawa. Ina ganin yanzu sun fara fahimtar matsalar da muke fuskanta.
"Mun yi imanin cewa ana yada mafi yawan bayanan da ke da kuskure ne saboda rashin cikakken fahimtar kabilun da muke da su da rikitarwar matsalar tsaronmu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Ministan ya kuma zargi wata ƙungiyar ‘yan aware da aka haramta a Najeriya da shirya yaɗa bayanan ƙarya ta hanyar wasu ‘yan Amurka domin bata sunan Najeriya.

Najeriya ta bukaci hadin kan Amurka

Duk da yake ya amince cewa har yanzu ana fuskantar ƙalubalen tsaro, Idris ya ce Amurka ta kasance abokiyar hulɗa mai muhimmanci a fannin yaki da ta’addanci kuma ya kamata wannan haɗin gwiwar ta ci gaba.

"Eh, muna da rikici a Najeriya, amma a baya gwamnatin Amurka ta taimaka wajen magance wannan matsala. Don haka muna kira gare su da su dawo su haɗa kai da mu don kawo zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasarmu,” in ji shi.
Shugaban Amurka da Bola Tinubu.
Hoton shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @RealDonaldTrump, @OfficialABAT
Source: Getty Images

Ministan ya kuma soki wasu bayanai da ake amfani da su a ƙasashen waje wajen goyon bayan ikirarin cewa ana zaluntar Kiristoci a Najeriya.

Idris ya bukaci ƙasashen duniya da su fahimci yanayin Najeriya da adalci, ba tare da fassara shi ta hanyar siyasa ko bangaranci ba, yana mai cewa abin da ake buƙata shi ne fahimtar juna da haɗin kai, ba rikici da ruɗani ba.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

Tinubu da Ribadu sun fara shan yabo

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar The Citizens Project ta yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.

Kungiyar ta yabi jagororin biyu ne bisa yadda suka kwantar da hankali da hikimar da suka nuna wajen daukar mataki kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump.

Ta kuma jaddada manufarta na hada kan yan kasa domin bunkasa zaman lafiya da kare martabar Najeriya a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262