Tashin Hankali: Matasa Sun Bankawa Shingen Binciken Hukumar 'Immigration' Wuta
- Ana fargabar wani jami’in hukumar shige da fice (NIS) ya harbi wata mata mai suna Hunsu Elizabeth a Igbogbele, Badagry
- A wani bidiyo da aka gani, matasa sun fusata bayan harbin, inda suka kone shingen bincin hukumar shige da fice da ke yankin
- Dan majalisar tarayya, Sesi Whingan ya yi Allah wadai da lamarin, yayin da har yanzu NIS ba ta ce uffan kan batun ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Rikici ya tashi a Igbogbele, cikin ƙaramar hukumar Badagry ta Yammacin jihar Legas, bayan da wani jami’in 'immigration' ya harbi wata mata, Hunsu Elizabeth.
An ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kuma ya tayar da hankalin matasan yankin da suka fusata suka kona shingen binciken hukumar da ke yankin.

Source: Twitter
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa mazauna yankin sun zargi jami’an da sakaci da kuma amfani da bindiga ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan
Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an Immigration sun harbi wata mata
A wani bidiyon da aka samu a ranar Litinin, an ga wuta mai ƙarfi tana cin ofishin hukumar, yayin da matasa ke ihu suna caccakar jami’an da suka yi harbin.
Duk da cewa ba a tabbatar da dalilin harbin ba, wasu faya-fayan bidiyo sun nuna yadda mazauna yankin ke taimakawa wajen ɗaukar matar zuwa asibiti, yayin da wasu ke ƙoƙarin hana jami’an tserewa daga wurin.
An ji wata mata a cikin bidiyon ta na cewa:
“Kun harbi matar! Kada ku tsere! Sun harbeta a hannu, bai kamata ku yi harbi ba!”
Sai wani mazaunin yankin ya ƙara da cewa:
“Ba za ku tsere ba! Ga abin da kuka jawo — harbin nan ya jikkata ta!”
An kuma nuna jami’an shige da fice akalla bakwai da ke ɗauke da bindigogi suna fuskantar turjiya daga jama’a yayin da suke ƙoƙarin shiga motarsu su 'tsere'.
Dan majalisa ya yi Allah wadai da harbin
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Badagry, Sesi Oluwaseun Whingan, ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin, inda ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, dan majalisar ya ce:
“Na karɓi labarin wannan mummunan lamari da ya faru a Igbogbele inda wani jami’in hukumar shige da fice ya harbi Hunsu Elizabeth a lokacin da take cikin gidanta.
"Muna godewa Allah cewa ta tsira daga wannan harbi, kuma ina roƙon Ubangiji ya ba ta lafiya cikin gaggawa.”
Ya ƙara da cewa wannan lamari “mai tayar da hankali ne,” yana mai cewa ba shi ne karo na farko ba da al’ummar Badagry ke fuskantar irin wannan barazana daga jami’an tsaro da ke aiki a kan hanyar Badagry–Owode–Seme ba.

Source: Original
Hukumar Immigration ta yi shiru kan batun
A halin yanzu, mai magana da yawun hukumar shiga da ficen Najeriya (NIS), Akinsola Akinlabi, bai amsa kira ko saƙonnin da aka aika masa don jin ta bakinsa ba.
Rahotanni sun ce an kwashe matar zuwa asibiti inda take samun kulawar likitoci, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin daidaita al’amura a yankin domin guje wa ƙarin tashin hankali.
Tinubu ya nada sabuwar shugabar NIS
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya nada DCG Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS).
DCG Kemi Nandap ta karbi ragamar shugabancin NIS daga hannun Wura-Ola Adepoju, wadda wa'adin aikinta ya kare a ranar 29 ga Fabrairu, 2024.
Tinubu yana da yakinin cewa sabuwar shugabar za ta karfafa gyare-gyaren da ake yi a NIS tare da samar da ingantacciyar hanyar isar da aiki mai inganci ga ‘yan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

