Tinubu Ya Tura Manyan Kusoshi zuwa Landan, An Fara Kokarin Dawo da Sanata Ekweremadu Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da Birtaniya domin dawo da Sanata Ike Ekweremadu gida Najeriya ya karisa hukuncinsa
- Shugaba Tinubu ya tura tawagar manyan kusoshin gwamnati domin duba yiwuwar musayar fursunoni bisa dokokin Birtaniya
- Kotun Landan ta daure tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawan bayan kama shi da laifin cire sassan jikin dan adam
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara kokarin samar wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu sassauci bayan Birtaniya ta daure shi.
Gwamnatin Tinubu na kokarin bin hanyoyin diflomasiyya domin maido da sanatan daga gidan yarin Birtaniya zuwa gidan gyaran hali a Najeriya don ci gaba da zaman hukuncinsa.

Source: Twitter
Tinubu ya tura tawaga zuwa Landan
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wata tawaga mai ƙarfi daga Najeriya ta isa ƙasar Birtaniya a ranar Litinin domin tattaunawa da hukumomin ƙasar kan wannan batu.

Kara karanta wannan
Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu suka bullo wa barazanar harin Amurka sun fara jan hankali
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar ta kunshi Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, da kuma Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, inda suka gana da jami’an Ma’aikatar Shari’a ta Birtaniya a birnin Landan.
Daga bisani, tawagar ta kai ziyara ofishin jakadancin Najeriya da ke Landan, inda Ambasada Mohammed Maidugu, wanda ke rikon mukamin Jakadan Najeriya a Birtaniya, ya tarbe su.
Ana kokarin sassauta wa Sanata Ekweremadu
A cewar majiyoyi masu tushe, wannan tattaunawa na daga cikin ƙoƙarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi domin ganin an samu sassauci ko sake duba hukuncin Ekweremadu bisa dalilai na jin ƙai da na doka.
Wani babban jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ya tabbatar da cewa gwamnati tana kokarin tattaunawa da hukumomin Birtaniya kan yiwuwar musayar fursunoni ko belin jin ƙai bisa tsarin dokokin ƙasar.
“Muna aiki kan yiwuwar musayar fursunoni domin ya dawo Najeriya ya kammala sauran wa’adin hukuncinsa anan gida, yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu,” in ji shi.

Source: Twitter
Wane hukunci aka yanke wa sanatan a Landan?
Sanata Ike Ekweremadu, wanda ya shafe shekaru da dama a majalisar dattawa, ya rike kujerar Mataimakin Shugaban Majalisa har sau uku.
An same shi da laifin hada baki wajen safarar wani saurayi dan Najeriya, David Nwamini, da nufin cire masa koda tare da sanyawa diyarsa mai fama da ciwo.
Kotun Landan ta yanke masa hukuncin shekaru tara da watanni takwas a gidan yari a watan Maris 2023, tare da matarsa Beatrice, da likita Dr. Obinna Obeta, in ji rahoton The Sun.
Tinubu na goyon bayan kafa Anioma
A wani rahoton na daban, kun ji cewa Sanata Ned Nwoko ya yi ikirarin cewa shigaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na goyon bayan kudirin kirkiro jihar Anioma a Kudu maso Gabas.
Sanata Nwoko ya ce sanatoci 97 sun riga sun sanya hannu kan takarda da ke goyon bayan kafa jihar Anioma, abin da ya kira matakin da bai taɓa faruwa ba a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan
Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya
Ya kara da cewa shirin ya samu goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kuma Shugaba Tinubu ya nuna cewa zai rattaba hannu a kafa jihar da zarar an kammala bin matakan doka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
