Yadda Wuta Ta Tashi a Kasuwar Kano, Ana Fargabar Ta Lalata Shaguna sama da 40
- Wata gobara ta da ta tashi da safiyar 10 ga Nuwamba, 2025 a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke jihar Kano ta jefa 'yan kasuwa a cikin dimuwa
- Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar faruwar lamarin, inda ta yi zargin cewa lamarin ya sakamakon kuskuren amfani da makunnin wuta
- Ginin mai hawa ɗaya da shaguna sama da 40 ne ya kama da wuta, lamarin da ya sa aka nemi ahajin jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Darakta, Alhaji Sani Anas, ta tabbatar da afkuwar wata gobara a kasuwar Singa.
Gobarar ta afku a kasuwar da ta yi shura wajen cinikayyar kayayyakin masarufi da 5.00 na safe, inda wani bawan Allah, Mubarak Muhammad ya kira jami'an hukumar.

Kara karanta wannan
EFCC ta baza komarta, ta nemi taimakon FBI da Interpol don cafke tsohon gwamna, Timipre Sylva

Source: UGC
A karin bayanin da Legit ta samu, hukumar ta ce jami'anta daga sassa daban-daban na hukumar sun garzaya zuwa wurin cikin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gobara ta tashi a Kano
Daily Post ta wallafa cewa Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce a lokacin da jami'amsu suka isa wurin, sun tarar da wani gini mai hawa ɗaya yana ci da wuta.
Ya tabbatar da cewa wutar na ci a ginin Gidan Alhaji Abdulmunafi Yunusa, kuma ta lalata shaguna 25 na wucin gadi da ke gaban ginin, da kuma shaguna 19 daga saman bene.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, jami’an hukumar sun yi nasarar rage barnar ta yadda shaguna 24 daga saman bene ba su ƙone ba.
Dalilin tashin gobara a Kano
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, jami’an hukumar sun yi nasarar rage barnar ta yadda shaguna 24 daga saman bene ba su ƙone ba.

Kara karanta wannan
Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025
Ya bayyana cewa sai dai sun fuskanci cikas sakamakon tireloli da aka ajiye ba daidai ba da suka toshe hanya.

Source: UGC
A cewarsa:
"Jami'anmu sun samu matsaloli da dama wajen samun hanyar shiga wannan gida, a sakamakon ajiye manyan motoci da ake yi a kan hanya. Wannan ya hana motar hukumar shiga wannan wuri domin kai daukin gaggawa."
"Bayan haka kuma mun samu ganaw ad amutane biyu daga cikin wadanda suke kula daga wannan wuri, Akwai shugaban wannan gida, Ambasada Garba Ibrahim Mai Maggi da kuma Mai gadin wannan wuri, Malam Ibrahim.:
"Sun tabbatar mana da cewa, wannan gida na amfani da makashin wuta guda daya, wanda idan an kashe shi, dukkanin gidan za su rasa wuta."
Ya tabbatar da cewa sun gano ba da zarar an kammala kasuwanci ne ake kashe wutar ba, har sai kowa ya tashi. Ya ce sun yi zargin ba a y amfani da makashin wutar yadda ya kamata ba.
Gobara ta jawo asara a Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa gobara ta tashi a kasuwar wayoyi da ke Kano a safiyar ranar babbar Sallah, inda ta lalata shaguna da dama tare da jawo asarar miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan
Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji
Lamarin ya fara jawo hankalin jama’a ne bayan wani mutum ya wallafa bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna hayaki mai yawa na tashi daga wani bangare na kasuwar.
Wani ɗan kasuwa a Farm Centre mai suna Muhammad Daula ya bayyana cewa mafi yawan masu shaguna ba su je kasuwa ba a ranar saboda bikin Sallah yayin da abin ya faru.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng