Matsalar Sufurin Amurka Ta Yi Kamari, Trump Ya Yi wa Ma'aikata Barazana
- Shugaba Donald Trump ya yi barazanar rage albashin masu kula da zirga-zirgar jiragen sama da suka daina zuwa aiki
- Kungiyar kwadago ta NATCA ta kare mambobinta tana cewa sun kokarin aiki ba tare da albashi ba tsawon kwanaki 40
- Akalla tashin jirage 2,300 aka soke a ranar Litinin, yayin da fiye da jirage 8,700 suka yi jinkirin tashi a fadin Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Tashin hankali ya karu a fannin zirga-zirgar jiragen sama a Amurka bayan Shugaba Donald Trump ya yi barazanar rage albashin masu kula da zirga-zirgar jirage.
Trump ya yi barazanar ne ga ma'aikatan da suka ki zuwa aiki yayin da gwamnatin kasar ke cigaba da zama a rufe.

Source: Getty Images
A ranar Litinin, an soke sokin tashin jirage 2,300 yayin da Trump ya bayyana a shafinsa na Social Truth cewa zai hukunta duk wanda da ya ki komawa aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya ce zai iya ba ma'aikatan da suka cigaba da aiki kyautar $10,000 da maye gurbin wadanda suka ga sun gaji da aiki wa gwamnatin Amurka.
Martanin kungiyar NATCA ga Trump
Kungiyar kwadago ta masu kula da zirga-zirgar jiragen sama, NATCA, ta soki furucin shugaban, tana mai cewa mambobinta jarumai ne da ke ci gaba da aiki ba tare da albashi ba.
A cikin wata sanarwa, Times of India ta rahoto kungiyar ta ce:
“Ya isa haka.”
Ta bukaci majalisar dokoki da ta kawo karshen rufe gwamnati da ta kai kwanaki 41, wacce ta zama mafi tsawo a tarihin Amurka.
Shugaban kungiyar, Nick Daniels, ya bayyana wata yarjejeniya da ke fitowa daga majalisar dokoki a matsayin “mataki mai kyau” don kawo karshen rikicin.
“Bai kamata masu kula da zirga-zirgar jiragen sama su zama ana musu kallon siyasa ba lokacin da gwamnati ta tsaya,”
Inji Daniels, wanda ya jaddada cewa ma’aikatan sun dade suna aiki a mawuyacin hali.
Matsalar jiragen sama a Amurka
Rahotanni sun nuna cewa tun kafin matsalar tsarin kula da zirga-zirgar jiragen sama yana fuskantar matsaloli saboda karancin ma’aikata.
A halin yanzu kuma, adadin fasinjoji na karuwa yayin da bukukuwan karshen shekara ke kara gabatowa.

Source: Getty Images
Baya ga tashin jirage 2,300 da aka soke a ranar Litinin, fiye da jirage 8,700 sun yi jinkirin tashi a filayen jiragen sama, kuma an soke tashin jirage 1,100 da aka tsara za su tashi a yau Talata.
A makon da ya gabata, gwamnatin Trump ta umarci rage kashi 10 cikin 100 na zirga-zirgar jirage a filayen jiragen sama da dama saboda karancin ma’aikata.
Martanin majalisar dokokin Amurka
Dan majalisar wakilai na jam’iyyar Democrat, Rick Larsen, ya soki kalaman Trump yana cewa ba su da kan gado.
Ya kara da cewa:
“Ya kamata mu godewa mata da maza da ke aiki suna tabbatar da cewa jiragen sama suna tafiya lafiya, ba mu rika sukar su ba.”
Amurkawa sun shiga tsaka mai wuya
A wani labarin, mun kawo muku cewa rufe gwamnatin Amurka ya jefa dubban mutane cikin wahalar rayuwa.
Baya ga matsalar sufuri, lamarin ya shafi tallafin abinci da gwamnatin kasar ke ba marasa karfi domin rage musu radadin rayuwa.
Shugaba Donald Trump ya ce ya dakatar da tallafin abincin har zuwa lokacin da za a shawo kan rufe gwamnati da aka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


